Jump to content

Saminu Ɗorayi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saminu Ɗorayi
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 1940 (83/84 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Liman


Malam Saminu Dorayi Babba limamin masallacin Dorayi Babba dake jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya.

Malam Saminu Ibrahim Ɗorayi wanda akafi sani da Malam Saminu Ɗorayi, (an haife shi ne a birnin Kano a shekarar 1940). shi ne babban limamin masallacin Ɗorayi Babba a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.[1]

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Saminu an haife shi a Kano a shekarar 1940. Ya rayu tare da mahaifinsa (wato Malam Ibrahim Ɗorayi babba) ya kuma fara karatu a wajen mahaifinsa har ya sauke Al-Ƙur'ani mai tsarki kafin rasuwar mahaifinsa. Mahaifinsa ya rasu a shekara ta 1959. Bayan rasuwar mahaifinsa ya koma karatu wurin almajiran mahaifin sa inda ya koyi Ilimin fikihu da Ilimin tafsiri dana Hadisi.[2]

Karatun Boko

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan wasu lokuta malam yaga cewar bayajin dadin irin kallon da akeyiwa malaman soro wato ana musu kallon kamar su ba komai bane. Wannan tasa ya shiga SAS (kwalejin harshen Larabci). Bayan ya gama kuma ya shiga Jami'ar Bayero, inda a nan ya yi difiloma da digiri baki daya.

  1. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gxgqn3p0jo
  2. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gxgqn3p0jo