Samuel A. Ilori
Samuel A. Ilori | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 11 ga Janairu, 1945 (79 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Oxford |
Thesis director | Aubrey William Ingleton (en) |
Dalibin daktanci |
Deborah Olayide Ajayi (en) Bamidele Ayodeji Oluwade (en) Michael O. Ajetunmobi (en) Hammed Praise Adeyemo (en) |
Sana'a | |
Sana'a | masanin lissafi |
Employers | Jami'ar Ibadan |
Kyaututtuka | |
Mamba | Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Samuel A. Ilori malami ne dan Najeriya a fannin lissafi a tsangayar lissafi ta Jami'ar Ibadan Najeriya.[1] Ya kasance tsohon shugaban Sashen Lissafi, Shugaban tsangayar lissafi, tsohon Provost na Kwalejin Kimiyya da Fasaha, kuma tsohon Shugaban Kungiyar Lissafi ta Najeriya. Shi ma memba ne na Kwalejin Kimiyya ta Afirka.[2]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ilori a ranar 11 ga Janairu 1945. Ya sami digiri na farko, B.Sc. a fannin lissafi tare da karramawar ajin farko a shekarar 1968 daga Jami'ar Ibadan dake Najeriya. Daga nan sai ya koma kasar Ingila inda ya sami Diploma a Advanced Mathematics a shekarar 1969 daga Jami’ar Oxford, sannan a shekarar 1972 ya samu digirin digirgir na D.Phil. digiri a fannin lissafi daga jami'a guda.[3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ya kasance shugaban sashen Physics da Mathematics daga 1977 – 1979. Daga baya, ya ci gaba da zama shugaban tsangayar ilimi a shekarar 1990 da kuma Provost of Science and Technology a 1994. A 2003, ya zama shugaban sashen lissafi.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "SA.ILORI | Faculty of Science, UI". sci.ui.edu.ng. Retrieved 2022-06-29.
- ↑ "Ilori Samuel A. | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 2019-10-26. Retrieved 2022-06-29.
- ↑ 3.0 3.1 "Prof. S. A. Ilori – Member - Ajayi Crowther University, Oyo" (in Turanci). 2013-02-20. Retrieved 2022-06-29.