Jump to content

Sani Aliyu Dandawo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sani Aliyu Dandawo Ya Kuma kasance mawakin Hausa ne, na gargajiya. Shahararre ne a fanin waka, An haife shi a Argungu da ke jihar Kebbi.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifa Sani Aliyu Dandawo a kasar jihar Sokoto, a Najeriya. Ya fara waka ne a shekarar 1964 inda ya maida hankali akan wakokin fada, daga baya ya fara wake attajirai da yan siyasa.[1] Alhaji Sani Aliyu Dandawo dai na cikin fitattun makadan fada wadanda suka dauki lokaci mai tsawo tauraronsu na haskawa a kasar Hausa, inda ya kwashe fiye da shekaru hamsin yana waka.[2]