Jump to content

Saniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saniya
organisms known by a particular common name (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na livestock (en) Fassara, Shanu, domesticated mammal (en) Fassara da captive mammal (en) Fassara
This taxon is source of (en) Fassara fata
saniya na kwance
fulani na kiwon shanu
saniya mai gashi
Saniya fara da bakaa


Shanu, namiji:Sa, tamace: Saniya, karami:dan maraki, babba:Bijimi, kalman shanu kuma shine gama-garin jinsi, dabbace mai Kafafuwa guda hudu 4, mutane suna amfani da dabban domin ayyukan gona,dana cikin gari. kamar huda, haro, da kuma daukar kaya,dakuma harp, kuma suna samun nama, taki, madara da kuma magani daga jikin dabban. Shanu dabbace wacce mahauta suke yawan safaranta saboda tana daga cikin dabbobi da akafi yawan cin namansu a duniya, akan sarrafa naman ta wajen girke girke daban daban, naman shanu tana daga cikin nama masu dadi da kuma gina jiki.[1][2] Akan sarrafa nonon da ake tatsa ajikin shanun ta hanyoyi daban daban kamar su yogot akan fidda Mai acikin nonon da sauran su, sannan akan sha nonon shanun da fura ko kuma danbu, akan sha wasu magunguna na gargajiya da nonon shanun.

Ana yin kiwon saniya a gida ana iya yin sa a cikin daji,ako ina ana iya kiwon saniya indai gurin ya kasance ya na da koriyar ciyawa ko busassa

Dabbace wacce ake tatsan madara a hantsan ta.

Ana amfani da shanu a gonaki domin yin huda.

Tseren Shanu kenan a wani gari mai suna Pacu-Jawi dake cikin yammacin kasar Indonesiya, ana yin tseren ne a cikin tabo

Ana amfani da shanu wajen yin wasannin gargajiya, kaman hawan kaho, tsere da dai sauransu.

  1. "FAO – News Article: Key facts and findings". www.fao.org (in Turanci). Archived from the original on 1 January 2019. Retrieved 4 June 2021.
  2. "Treating beef like coal would make a big dent in greenhouse-gas emissions". The Economist. 2 October 2021. ISSN 0013-0613. Retrieved 3 November 2021.