Jump to content

Sheik Umar Futi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
JS_Icon_Edit
JS_Icon_Edit

Sheikh Umar Futi

An haifi El-hadj Umar bin Sa'id Al-futy a garin Futa-toro na kasar Senegal a bangaren da akewa lakabi da Sene-Gambia, 9 ga watan Maris a shekarar 1796. Ya mutu a 12 ga watan Faburairu, a shekarar 1864 a Bamadiagana, Mali. Yayi karatun addini a gaban iyayensa da yan'uwansa, domin dama gidan su gidan karatu ne.

Asalinsa Shi Batorankene wato (turubbe) Wata nasabace Daga Cikin qabilar fulbe Inda yafito tsatso Daya da Sheikh Usman Bin Fodio wato torankawa.[TAJAsPkjwZVWVG9xFT4A9uYfGCx86ax3Uw 1]


A shekarar 1828, sai ya tafi aikin hajji, ya dawo a shekarar 1830. A kan hanyarsa ta dawowa, ya tsaya a garin Dimashka na lokacin mai suna Ibrahim Pasha.


Ya taba zuwa sakkwato ya dan zauna har ya auri 'yar Sarkin Muslim Muhammad Bello. A shekarar 1848, ya kaddamar da jihadinsa tare da goyan bayan dinbim almajiransa. Ya samu nasarar musuluntar da mutanen daular Melinke, har ya tsallaka garin Kayes dake ksar Mali a yanzu. Akwai labarin dake cewa har yanzu 'yan yawon bude ido suna ziyartar ganuwar da ya ginawa garin.

Wasu daga cikin danginsa har yanzu suna zaune a cikin wannan yanki har suka kafa garin Yallemeta da Hadeja. Wannan nema yasa har yanzu ake ganin wasu mutanen a wannan yankin kaman Larabawa ko Fulani Gambiya.

== Manazarta==
[gyara sashe | gyara masomin]

[1]

  1. https://standard.gm/profile-in-faith/el-hadj-umar-tall-1797-1864-islamic-scholar-and-empire-builder/


Cite error: <ref> tags exist for a group named "TAJAsPkjwZVWVG9xFT4A9uYfGCx86ax3Uw", but no corresponding <references group="TAJAsPkjwZVWVG9xFT4A9uYfGCx86ax3Uw"/> tag was found