Jump to content

Sidi Muhammadu Baƙir na Durchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sidi Muhammadu Baƙir na Durchi
grand ayatollah (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Dorcheh (en) Fassara, 1847
ƙasa Iran
Mutuwa Dorcheh Piaz (en) Fassara, 1923
Makwanci Isfahan
Takht-e Fulad (en) Fassara
Kazeruni Tekiyeh (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Mortaza' Dorcheh'i
Ahali Mohammad Hossein Durchih'i (en) Fassara da Mehdi Durchih'i (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta Najaf Seminary (en) Fassara
Isfahan Seminary (en) Fassara
Malamai Mirza Shirazi (en) Fassara
Habibullah Rashti (en) Fassara
Hossein Kuh-Kamari (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Malamin addini
Wurin aiki Isfahan Seminary (en) Fassara da Nimavard Madrasa (en) Fassara
Muhimman ayyuka Mizan_ol_feqa'ha (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Shi'a

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i (1848-1923) Masanin Fikih da wanda ake koyi da shi a cikin addinin Shi'a

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i yana ɗaya daga cikin malaman addinin Shi’a a ƙarni na goma sha tara da ashirin, kuma malami ne a makarantar addinin Isfahan. Ya yi karatu a Najaf ƙarƙashin jagorancin Mirza Shirazi da Mirza Habibullah Rashti, kuma a Isfahan ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Baƙir Khansari. Daga cikin ɗalibansa akwai Sidi Abu al-Hasan Isfahani da Sidi Husain Brujerdi. [1]

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i an haife shi a shekara ta 1848 a ƙauyen Durche da ke Isfahan. Asalin zuri'arsa ya dawo ga Imam Musa al-Kadhim (a.s). Mahaifinsa shi ne Murtada, kuma 'yan uwansa Muhammadu Husain da Muhammadu Mahdi duk malamai ne. Mahdi ya yi karatu a Najaf kuma malami ne a makarantar addinin Isfahan. Kakansa, Muhammadu Mirluhi na Sabzawari, yana cikin manyan malamai a Isfahan a zamanin Safawiya kuma ya zamana da Muhammadu Taqi al-Majlisi. Durche'i ya rasu a shekara ta 1923 a Durche. An yi jana'izarsa daga Durche zuwa Isfahan kuma an binne shi a makabartar Takht-e Foulad.[2]

Wasu daga cikin manyan ɗaliban Ayatollah Durche'i sun haɗa da: Sidi Abu al-Hasan Isfahani, Sidi Husain Burujirdi, Mirza Hasan Jabiri Ansari, Mirza Ali Aqā Shirazi, Muhammad Hasan Aqā Najfi Qūchāni, Sidi Jamal al-Din Gulpaygani, Sidi Hasan Mudarris da Rahim Arbab.[3]