Jump to content

Sidi Muhammadu Baƙir na Durchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i (1848-1923) Masanin Fikih da wanda ake koyi da shi a cikin addinin Shi'a

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i yana ɗaya daga cikin malaman addinin Shi’a a ƙarni na goma sha tara da ashirin, kuma malami ne a makarantar addinin Isfahan. Ya yi karatu a Najaf ƙarƙashin jagorancin Mirza Shirazi da Mirza Habibullah Rashti, kuma a Isfahan ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Baƙir Khansari. Daga cikin ɗalibansa akwai Sidi Abu al-Hasan Isfahani da Sidi Husain Brujerdi. [1]

Sidi Muhammadu Baƙir na Durche'i an haife shi a shekara ta 1848 a ƙauyen Durche da ke Isfahan. Asalin zuri'arsa ya dawo ga Imam Musa al-Kadhim (a.s). Mahaifinsa shi ne Murtada, kuma 'yan uwansa Muhammadu Husain da Muhammadu Mahdi duk malamai ne. Mahdi ya yi karatu a Najaf kuma malami ne a makarantar addinin Isfahan. Kakansa, Muhammadu Mirluhi na Sabzawari, yana cikin manyan malamai a Isfahan a zamanin Safawiya kuma ya zamana da Muhammadu Taqi al-Majlisi. Durche'i ya rasu a shekara ta 1923 a Durche. An yi jana'izarsa daga Durche zuwa Isfahan kuma an binne shi a makabartar Takht-e Foulad.[2]

Wasu daga cikin manyan ɗaliban Ayatollah Durche'i sun haɗa da: Sidi Abu al-Hasan Isfahani, Sidi Husain Burujirdi, Mirza Hasan Jabiri Ansari, Mirza Ali Aqā Shirazi, Muhammad Hasan Aqā Najfi Qūchāni, Sidi Jamal al-Din Gulpaygani, Sidi Hasan Mudarris da Rahim Arbab.[3]