Sipho Owen Ndlovu (an haife shi a ranar 7 ga watan Oktoba 1994) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Zimbabwe wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ga kungiyar ƙwallon ƙafa ta Chicken Inn FC da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe.[1] Ya bugawa Bulawayo City FC wasa a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2018.