Sue Waddington
Sue Waddington | |||
---|---|---|---|
19 ga Yuli, 1994 - 19 ga Yuli, 1999 District: Leicester (en) Election: 1994 European Parliament election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Norfolk (en) , 23 ga Augusta, 1944 (80 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Leicester (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Kamsila | ||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Labour Party (en) |
Susan Waddington (an Haife ta a ranar 23 ga watan Agustan shekara ta alif dari tara da arbain da hudu 1944A.c) jami'ar ilimi ce ta Biritaniya kuma 'yar siyasa ta Jam'iyyar Labour wacce ta kasance memba a Majalisar Turai na Leicester.
An haife ta a Norfolk, Waddington ta halarci makarantar Blyth Grammar da Jami'ar Leicester. Ta yi aiki a matsayin jami'ar fannin ilimin manya, kafin ta zama mataimakiyar darakta a Derbyshire LEA, sannan a Birmingham LEA.[1]
A shekarar 1973, An zaɓi Waddington matsayin Majalisar gundumar Leicestershire, tana aiki har zuwa shekarar 1991, kuma ta kasance shugabar majalisa daga shekarar 1982 har zuwa shekara ta 1984. A zaben Majalisar Turai na shekarar 1994, an zabe ta don wakiltar Leicester, tana aiki har zuwa shekara ta 1999.[1]
Waddington ta kasance shugaban kungiyar Tarayyar Turai don Ilimin Manya [2] daga shekarar 2008 zuwa shekara ta 2013.
A halin yanzu ita ce (2019) kansila na gundumar Fosse a Majalisar Birnin Leicester[3] kuma ta kasance Mataimakiyar Magajin Garin a karkashin mulkinMagajin Garin Leicester Peter Soulsby.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 BBC-Vacher's Biographical Guide 1996. London: BBC Political Research Unit and Vacher's Publications. 1996. pp. 6–42. ISBN 0951520857.
- ↑ President: Sue Waddington. EAEA. Retrieved 2011-01-16.
- ↑ "Councillor Susan Waddington". Leicester.gov.uk. Retrieved 15 December 2019.