Jump to content

Sufurin Jirgin kasa a Lesotho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sufurin Jirgin kasa a Lesotho
rail transport by country or region (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara rail transport (en) Fassara
Ƙasa Lesotho
Tashar Maseru
Injin dizal tare da keken kaya na Lesotho Flour Mills a tashar Maseru

Kasar Lesotho tana da tashar jirgin kasa guda daya, dake Maseru babban birnin kasar. Ita ce ƙarshen layin reshen Maseru, wanda ke haɗuwa da layin dogo na Afirka ta Kudu.

Tsawon layin da ke cikin Lesotho, daga gadar kan iyaka akan kogin Mohokare zuwa tashar, 1.6 kilometres (1.0 mi) . An buɗe a ranar 18 ga watan Disamba, 1905.[1] Nisan layin dogo daga Maseru zuwa babban layin da ke Bloemfontein shine 137 kilometres (85 mi)

Tun daga shekara ta 2008, an yi ta tattaunawa kan gina sabbin hanyoyin jirgin ƙasa don haɗa Lesotho zuwa Durban da Port Elizabeth.[2]

  1. Boonzaaier, J.N.C (2008). Tracks Across the Veld. p. 245. ISBN 978-0-620-41711-2
  2. Radebe, Jeff (20 November 2007). Keynote address at the African Union Rail conference (Speech). Johannesburg. Retrieved 14 October 2010.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Media related to Rail transport in Lesotho at Wikimedia Commons