Tarihin Waliyi dan Marina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

TARIHIN WALI DAN MARINA

Unguwar Masanawa da ke cikin birnin katsina unguwa ce mai dimbin tarihi kuma sananniya ce saboda a nan ne manyan Waliyai masu karamomi suka wanzu a karni na goma sha bakwai (17th Century).

Waliyan su ne Wali Dan-Marina da kuma Wali Dan-Masani. Tarihi ya nuna cewa cikakken sunan wali Dan Marina shi ne Muhammad Ibn al-Sabbagh. Tarihi ya nuna cewa mahaifinsa balarabe ne wanda ya taso daga gabas ya kuma sauka a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya a gidan wani malami kuma attajirin arini mai suna Kayaba. Wannan marini an ce shi ne yake yi wa Sarkin Katsina na wancan lokacin Mamuda da iyalinsa rinin tufafinsu.

Ana nan sai wata rana mahaifin wali Dan-marina ya ga ‘yar Sarki Mamudu wadda ake kira da Baraka, ya ji kuma ta kwanta masa. A haka ne ya nemi aurenta, sai aka aura masa ita a kan sadaki zinare shida, suka kuma tare a gidan kayaba.

[1]

  1. https://www.muryarhausa24.com.ng/2017/10/rayuwa-tarihin-wali-dan-marina.html?m=1