Tammy Abraham
Tammy Abraham | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Kevin Oghenetega Tamaraebi Bakumo-Abraham | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Camberwell (en) , 2 Oktoba 1997 (27 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta | Pimlico Academy (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 82 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 190 cm |
Kevin Oghenetega Tamaraebi Bakumo-Abraham (an haife shi 2 Oktoba 1997), anfi sanin sa da Tammy Abraham, shi ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne, wanda ke buga wa ƙungiyar wasan ƙasar ingila amatsayin mai wasan gaba striker da kuma ƙungiyar Kulub ta Chelsea.
Tammy yayayyan akademi ɗin Chelsea ne, Abraham ya fara buga wasansa na kwararru ne a 2016 sannan yaje aro a kulub ɗin Bristol City. Anan ne, ya samu cigaba da nasarori da dama, inda aka bayyana shi amatsayin, "Young Player of the Season" wato Gwarzon ɗan'wasa Matashi na shekara da kuma kyautar wanda yafi cin ƙwallaye, haka yazamar dashi ɗan wasan daya fara samun irin wannan nasara acikin shekara ɗaya. Ya kuma ƙara zuwa wani aro a ƙungiyar Swansea City sai dai ƙungiyar bata jima ba, ta koma baya, in da fit a daga fafatawa a gasar Premier League. Ya koma Aston Villa a shekarar 2018 inda ya zama ɗanwasa na farko tun 1977 daya ci adadin ƙwallaye 25 acikin kakan wasa ɗaya ma ƙungiyar.
Abraham ya wakilci ƙasar under-18 level, inda ya kasance daga cikin yan'wasan 2017 UEFA European Under-21 Championship a ƙasar Poland. Ya fara buga wasan sa na kwararru a ƙasar a watan Nuwanban shekara ta 2017.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]