Tarihin Ƙasar Falasɗinu
Tarihin Ƙasar Falasɗinu | |
---|---|
history of a country or state (en) | |
Bayanai | |
Facet of (en) | history of the Levant (en) da State of Palestine |
Ƙasa | State of Palestine |
Tarihin ƙasar Falasɗinu ya bayyana a matsayin wani juyin-juya-hali na Ƙasar Falasɗinu a yammacin gabar kogin Jordan da zirin Gaza. A lokacin wa'adin mulkin Biritaniya, an gabatar da tsare-tsare masu yawa na raba Palasɗinu amma ba tare da amincewar dukkan ɓangarorin ba. A shekara ta 1947, an kaɗa kuri'a ga shirin raba kasa na Majalisar Dinkin Duniya na Falasdinu. Shugabannin Hukumar yahudawa ta Falasɗinu sun amince da wasu sassan shirin, yayin da shugabannin Larabawa suka ƙi amincewa da shi. Shirin dai na yunƙurin kafa ƙasar Isra'ila a cikin wani yankin na ƙasar Falasɗinu wanda yahudawa suka mamaye, sai a wannan lokacin wannan ƙudurin bai samu ƙarɓuwa ba gun ƙasashen Larabawa sai dai daga baya yahudawa sunyi nasarar kafa ƙasar Isra'ila. Wadda da dama daga cikin ƙasashen Larabawa suke kallo a matsayin zalunci. Wannan ya haifar da Yaƙin 1947-1949 na Falasɗinu kuma ya jagoranci, a cikin 1948, don kafa ƙasar Isra'ila a wani ɓangare na Falasɗinu yayin da wa'adin ya zo ƙarshe.
Zirin Gaza ya kasance ƙarƙashin Masar, kuma gabar yammacin kogin Jordan ce ke mulkinta, kafin Isra'ila ta mamaye yankunan biyu a yakin kwanaki shida da aka fafata a shekarar 1967. Tun daga wannan lokacin ne ake ta shawarwarin kafa ƙasar Falasdinu wadda daman can akwaita kawai yahudawan duniya ne suka taru suka murƙusheta. A cikin 1969, alal misali, PLO ya ba da shawarar kafa ƙasa ta ƙasa a kan gabaɗayan tsohon yankin na Biritaniya. Isra'ila ta ƙi amincewa da wannan shawara, domin da ace ta kai ga hana Isra'ila mamayar da take yi han izuwa yanzu. Tushen shawarwarin na yanzu dai shi ne na samar da kasashe biyu kan ko dai wani ɓangare ko kuma baki ɗaya na yankunan Falasdinawa - yankin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan, ciki har da gabashin birnin Kudus da Isra'ila ta mamaye tun shekara ta 1967.