Tarila Thompson
Tarila Thompson | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Tarila Emmanuel Thompson |
Haihuwa | Lagos,, 14 ga Faburairu, 1968 (56 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, filmmaker (en) da mawaƙi |
IMDb | nm2141940 |
Tarila Emmanuel Thompson (an haife shi a watan Fabrairu 14, 1968) ɗan wasan kwaikwayon Najeriya ne, darekta, mai shirya fina-finai, marubuci kuma mawaƙi. Thompson ya fara aikinsa a shekara ta 1992 kuma ana yaba masa saboda rawar da ya taka wajen fara harkar fina-finai masu magana da Turanci a Najeriya da aka fi sani da Nollywood.
An san Thompson don Love without Language (1993), Die Another Day (2004), Passion and Pain (2004) da Church Business (2006). Bayan ya dauki huta daga yin fim, Thompson ya dawo a shekar 2012 don yin fim ɗinsa na baya-bayan nan In the Creek, fim ɗin da aka yiwa lakabi da mafi tsadar fitarwa a Afirka.[5] Fim din yayi magana akan radadin da yan Neja-Delta ke ciki a Najeriya. A matsayinsa na mawaƙi, shi ne mamallakin El-Montage Records, lakabi rikodin kiɗa.
Rayuwa da matakin Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Thompson a Legas, Najeriya. Ya fito daga jihar Bayelsa, jiha ce a yankin Neja-Delta. Thompson ya sami digiri na farko daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha, Port-Harcourt. Yana auren Funto Diseye Thompson kuma yana da yara uku.[1] [2] [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://www.daylight.ng/daylight nollywood-personality-of-the-day-tarila-thompson Archived 2016-04-12 at the Wayback Machine
- ↑ https://www.pressreader.com/nigeria/thisday/20170225/282033326970800
- ↑ https://www.imdb.com/name/nm2141940/bio