An gudanar da taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 1998, a watan Nuwamba 1998 a Buenos Aires, Argentina.[1] Taron ya haɗada taron kasashe karo na 4 (COP4) ga tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (UNFCCC). An yi tsammanin za'a kammala sauran batutuwan da ba'a warware su ba a Kyoto a wannan taron. Duk da haka, rikitarwa da wahalar samun yarjejeniya a kan waɗannan batutuwa sun kasance ba za a iya warwarewa ba, kuma a maimakon haka ɓangarorin sun amince da "Shirin Aiki" na shekaru 2 don cigaba da ƙoƙari da kuma tsara hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar Kyoto, wanda za'a kammala nan da shekara ta 2000. A yayin taron, kasashen Argentina da Kazakhstan sun bayyana aniyarsu ta daukar nauyin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, ƙasashe biyu na farko da ba na Annex ba.