Taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 2004
Taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na 2004 | ||||
---|---|---|---|---|
United Nations Climate Change conference (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Argentina | |||
Kwanan wata | 6 Disamba 2004 | |||
Lokacin farawa | 6 Disamba 2004 | |||
Lokacin gamawa | 17 Disamba 2004 | |||
Shafin yanar gizo | unfccc.int… | |||
Wuri | ||||
|
An gudanar da taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya na shekara ta 2004 tsakanin (6 ga Disamba zuwa 17 ga Disamba, 2004), a Buenos Aires, Argentina. Taron ya haɗada taron ƙasashe karo na 10 (COP10) ga yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (UNFCCC).[1]
Ɓangarorin sun tattauna irin cigaban da aka samu tun bayan taron farko na sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya shekaru goma da suka gabata da kuma ƙalubalen da zai fuskanta a nan gaba, tareda mai da hankali musamman kan dakile sauyin yanayi da daidaitawa. Don haɓɓaka ƙasashe masu tasowa mafi dacewa da sauyin yanayi, an ɗauki Buenos Aires Plan of Action. [2] Ɓangarorin sun kuma fara tattaunawa kan tsarin bayan Kyoto, kan yadda za'a ware wajibcin rage fitar da hayaƙi bayan shekarar 2012, lokacin da wa'adin farko ya kare.[3]