Tashar Bas ta TBS

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tashar Bas ta TBS
Wuri

Tashar Bas ta Tafawa Balewa Square wacce kuma aka fi sani da Tashar ta TBS dake tsakiyar Lagos Island, Jihar Legas, Kudu maso Yamma, Najeriya . Tashar bas tana kan titin Massey Bamgbose 45/57, Legas Island.

Tashar bas ta TBS ta hada da filin Tafawa Balew da aka gina a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da biyu 1972 domin murnar samun 'yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban a shekara ta alif ɗari tara da sittin1960. A ranar 18 ga Maris, 2016, gwamnatin Akinwumi Ambode, tsohon gwamnan jihar Legas, ta kammala shirye-shiryen sake farfado da tashar don "kara inganta aikin babban birni na jihar". An ƙaddamar da sabon tashar a cikin 2017.

Hanyoyi[gyara sashe | gyara masomin]

  • TBS - CMS
  • TBS - Ikeja, Barracks
  • TBS - Ajah, Hanyar Lekki
  • TBS - Oshodi
  • TBS - Berger
  • TBS - Leventis
  • TBS - Fadeyi
  • TBS - Ikorodu

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Samfuri:Lagos