Jump to content

Tattaunawar user:Iliyabarnabas

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa![gyara masomin]

Ni Robot ne ba mutum ba.

Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Iliyabarnabas! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma muna fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial. Na gode. AmmarBot (talk) 21:26, 6 Satumba 2023 (UTC)[Mai da]

Al'ummar Unguwar Kerau dake Mazaɓar Gabas2 cikin Garin Katsina, sun yi kira ga Shugaban Hukumar SEPA Alh. Kabir Usman Amoga, da ya dubi Girman Allah ya cika Alkawarin da yayi masu na kauda sharar da aka fiddo, sakamakon aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwa da Matasan Unguwar suka gudanar, domin kaucewa Ambaliyar ruwa a ƴan kin. Wata Sanarwa daga Ƙungiyar Cigaban yankin ta bayyana cewar, biyo bayan aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwa, da Matasan yankin sukai, ya sa suka roki Shugaban Hukumar na SEPA, Alh. Kabir Usman daya samar masu da Motocin da zasu kauda Sharar da suka fiddo, domin gudun kada Sharar ta sake komawa a cikin hanyoyin ruwan da aka fiddo ta, Saboda da ruwan Sama da ake samu. Sanarwar ta ce, duk da alkawarin Motocin da Sabon Shugaban Hukumar, kuma Haifaffen yankin Alh. Kabir Amoga ya yi masu, da zarar sun kammala aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwan, sai dai har yanzu kusan kwanaki uku kenan, don haka sukai tuni akan wannan alkawari, domin ɗaukar matakin Gaggawa na kwashe kauda Sharar akai ta inda ya dace, domin gujewa aukuwar Ambaliyar ruwa a gidajen Al'umma. Tun a ranar Asabar din da ta gabata dai ne, Matasan Unguwar ta Kerau dake Layin Masallacin Juma'a, su ka ɗauki matakin yin aikin gyayya, domin tsaftace duk wasu hanyoyin ruwa dake yankin, tare da neman Ɗaukin Hukumar SEPA, na ta sa Motocin ta su kwashe sharar da aka fiddo, don haka suke yin kira ga Shugaban Hukumar da ya dubi wannan Lamari, domin kare dukiyoyi da kuma rayukan Al'umma.[gyara masomin]

Al'ummar Unguwar Kerau dake Mazaɓar Gabas2 cikin Garin Katsina, sun yi kira ga Shugaban Hukumar SEPA Alh. Kabir Usman Amoga, da ya dubi Girman Allah ya cika Alkawarin da yayi masu na kauda sharar da aka fiddo, sakamakon aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwa da Matasan Unguwar suka gudanar, domin kaucewa Ambaliyar ruwa a ƴan kin.

  Wata Sanarwa daga Ƙungiyar Cigaban yankin  ta bayyana cewar, biyo bayan aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwa, da Matasan yankin sukai, ya sa suka roki Shugaban Hukumar na SEPA, Alh. Kabir Usman daya samar masu da Motocin da zasu kauda Sharar da suka fiddo, domin gudun kada Sharar ta sake komawa a cikin hanyoyin ruwan da aka fiddo ta, Saboda da ruwan Sama da ake samu.
 
   Sanarwar ta ce, duk da alkawarin Motocin da Sabon Shugaban Hukumar, kuma Haifaffen yankin Alh. Kabir Amoga ya yi masu, da zarar sun kammala aikin gayyar tsaftace hanyoyin ruwan, sai dai har yanzu kusan kwanaki uku kenan, don haka sukai tuni akan wannan alkawari, domin ɗaukar matakin Gaggawa na kwashe kauda Sharar akai ta inda ya dace, domin gujewa aukuwar Ambaliyar ruwa a gidajen Al'umma.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata dai ne, Matasan Unguwar ta Kerau dake Layin Masallacin Juma'a, su ka ɗauki matakin yin aikin gyayya, domin tsaftace duk wasu hanyoyin ruwa dake yankin, tare da neman Ɗaukin Hukumar SEPA, na ta sa Motocin ta su kwashe sharar da aka fiddo, don haka suke yin kira ga Shugaban Hukumar da ya dubi wannan Lamari, domin kare dukiyoyi da kuma rayukan Al'umma. Iliyabarnabas (talk) 22:02, 6 Satumba 2023 (UTC)[Mai da]