Teemah Yola

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Fatima Isa Muhammad wacce aka fi sani da Teemah Yola Jaruma ce a masana'antar shirya fina-finai na Hausa wato Kannywood da ke arewacin Najeriya.[1] jarumar ta yi suna sanadiyyar wani fim mai dogon zango, mai suna labarina.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Fatima a watan mayu 11 ga watan a shekarar 1993 a cikin garin Yola jihar Adamawa Nijeriya. Mahaifin ta shi yasata a makarantar firamare, bayan ta gama sakandiri ta sami shiga Jami'ar Maiduguri inda ta karanci harshen larabci.[2]

Sana'ar fim[gyara sashe | gyara masomin]

Ta fara fitowa a wasan kwaikwayo tun a shekarar 2015 wanda yafi fito da ita shine fim din labarina Mai dogon zango

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi fina finai da dama, amman an santa a fim wanda fim din 'labarina', wani fim da Aminu Saira ke bayar da Umarni.[3]

Ga wasu fina-finai;[4]

  1. Labarina
  2. Ukku sau ukku
  3. Dakin Amarya
  4. Ragon Azanci
  5. Gida ukku
  6. Tozarci. da sauransu

Rayuwar sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Fatima tayi aure inda ta haifi yara guda biyu, [ana buƙatar hujja] daga Nan ta rabu da mijinta ta shiga harkar fim gadan-gadan.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]