Tijjani Faraga
Tijjani Faraga Jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya dade yana fim a masana'antar, Yayi fina finai da dama da yake taka rawa a fannin iyaye.[1] furodusa ne jarumi Kuma darakta.[2] ya yi fina finai da dama a masana'antar. Fitacce ne kuma sananne ga masu kallo.
Takaitaccen Tarihin Sa
[gyara sashe | gyara masomin]Tijjani Faraga jarumi Kuma furodusa ya shigo masana'antar Shekaru Sha hudu baya, Yana taka rawa a matsayin uba, Yaya, Dan uwa, Dan siyasa. Yana yin fim da turanci Yana Jin turanci sosai. Ya shigo masana antar fim da girman sa , Yana da mata da yara. Yana fim a Nollywood fina finan turanci. Ya Yi fina finai da dama na Hausa Dana turanci a masana'antar fim ta kudancin Najeriya. Cikakken sunan sa shine Alhaji tijjani usman Faraga Yana da sarautar gargajiya inda aka nadashi zannnan dansararin sarkin bauchi.[3]