Tolu' A. Akinyemi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tolu' A. Akinyemi
Rayuwa
Karatu
Makaranta University of Hertfordshire (en) Fassara
Sana'a
Tolu A. Akinyemi - Zakin Newcastle
Tolu Akinyemi, aka The Lion of Newcastle, holding some of his books.
Tolu' A Akinyemi riƙe da wasu littafansa.

Tolu A. Akinyemi marubuci ne kuma mawaƙi ɗan Najeriya wanda ya sami lambar yabo da yawa da ya shahara dalilin kundin waƙoƙin sa, Dead Lions Don't Roar.[1][2][3]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Akinyemi Tolulope Adeola Akinyemi a Ado-Ekiti. Ya yi digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Jihar Ekiti sannan ya yi digiri na biyu a fannin (Accounting and Financial Management) daga Jami’ar Hertfordshire, Hatfield, UK.[4]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Akinyemi ya tashi daga Najeriya zuwa Birtaniya a shekarar 2010 kuma tun daga nan ya buga littattafai guda ashirin da ɗaya.[5][6][7][8] Ya fito da littafinsa na farko na waƙa, mai taken; Dead Lions Don't Roar, a cikin shekaran 2017.[9]

Akinyemi ya fitar da, Dead Dogs Don't Bark , littafinsa na biyu na wakoki kuma littafi na uku a shekarar 2018.[10] Sai kuma Dead Cats Don't Meow, wanda aka saki a cikin Afrilu 2019 kuma ya ba da rangadin littattafai na ƙasashe da yawa na Birtaniya da Najeriya.[11]

An fitar da littattafan Akinyemi da aka buga/wallafa da kuma ta hanyar yanar gizo. An nazarta wakokinsa a matsayin “waqoqin daukaka” da mujallar Nazarin Turanci a Afirka, ta yi.[12]

Tarin waqoqin kundin Tolu, mai taken, Everybody Don Kolomental, an yi amfani da shi azaman hanyar koyarwa don shigar da ɗaliban likitanci a cikin tattaunawa game da lafiyar hankali da jin daɗin rayuwa a Jami’ar Benin/Asibitin Koyarwa, Jihar Edo, Najeriya.[13]

Har ila yau, waƙarsa, Everybody don Kolomental', an karanta tare da yin nazari daga Farfesa Kingsley Oalei Akhigbe, farfesa a fannin ilimin taɓin hankali, a cikin jerin lakcoci na farko na 293 a Jami'ar Benin, kan maudu'in, (Kolomental and Elephant) a cikin dakin. - (Our Mental Health).[13]

Akinyemi shi ma mawaƙi ne na wasan kwaikwayo kuma ya yi wasa a bikin, Great Northern Slam, Crossing The Tyne Festival, Feltonbury Arts and Music Festival,The Havering Literary Festival. Shine baƙon da de yi wasa a Havering Libraries Black History, a watan Oktoba 20121.[14] Haka-zalika, wani taro a Woolwich Centre Library National Poetry Day a watan Oktoban 2018; Yayi wasa a dandalin The Stanza - Inda yayi wasa, jawabi, wasan ban dariya, a Open Mic, wanda aka gudanar a ranar 31 ga Agusta 2023. Ya kasance mawaƙin baƙo a wurin taron Ndi Igbo North East England (NINEE) Black History Month.[15]

A ranar 25 ga Oktoba 2023, Lion & Lilac, ƙungiyar adabi wacce Akinyemi na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ta, ta shirya taron waƙa don murnar watan Baƙar fata.[16][17] Tolu ya kasance jarumin kanun labarai, tare da wasu hazikan mawaƙa.

A watan Satumbar 2023, Tolu Akinyemi ya fara rangadin waka na farko a fadin Arewa maso Gabashin Ingila, wanda ya soma da The Cooking Pot, a gidan Baba Yaga, Whitley Bay. Wannan ya biyo bayan wasan kwaikwayo mai ban sha'awa a Poetry Jam, wanda aka shirya a Cibiyar Waddington Street da ke Durham, tare da wasu fitattun wurare a faɗin yankin.

Majalisar Arts Council England ta amince da shi a matsayin marubuci mai hazaka ta musamman.[18][19]

Girmamawa da kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin 2020, ya sami kyautar, Best Indie Book Award, sakamakon kundin waƙarsa, ƘA Booktiful Love.[20] Tarin gajerun labaran waƙoƙinsa, Inferno of Silence, ya lashe lambar yabo ta 2021 IRDA Kyautar, Discovery Award,[21] dalilin gajerun labarai da Next Generation Indie Book Awards Archived 2020-06-26 at the Wayback Machine (2021) dalilin, Best Cover Design (Fiction).[22]

Tallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

Tun a shekarar 2017, Akinyemi ya ba da gudummawar wani kaso daga cikin kuɗaɗen da aka samu daga littafansa na sadaka. Ya bayar da gudummawar tallafi £1000, ga, Age Uk Northumberland's friendship line campaign.[23][24][25]

Bibliography[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Suna Mawallafi ISBN Iri
August 2017 Dead Lions Don't Roar: A Collection of Poet Fic Wisdom For The Discerning The Roaring Lion Newcastle I978-1-999815905[ Poetry
April 2018 Unravel Your Hidden Gems T & B Global Concepts Ltd 1999815998 Nonfiction
September 2018 Dead Dogs Don't Bark T & B Global Concepts Ltd 978-1999815929 Poetry
April 2019 Dead Cats Don't Meow – Don't waste the ninth life T & B Global Concepts Ltd 9781999815943 Poetry
August 2019 Never Play Games With the Devil The Roaring Lion Newcastle 9781999815967 Poetry
May 7 2020 Inferno of Silence   The Roaring Lion Newcastle 9781913636029 Short stories
May 8 2020 A Booktiful Love The Roaring Lion Newcastle 9781913636005 Poetry
January 1 2021 Black # Inferior   The Roaring Lion Newcastle 978-1913636067 Poetry
January 1 2021 Never Marry A Writer The Roaring Lion Newcastle 978-1913636081 Poetry
April 1 2021 Everybody Don Kolomental The Roaring Lion Newcastle 978-1913636111 Poetry
June 1 2021 I Wear Self-Confidence Like a Second Skin The Roaring Lion Newcastle 978-1913636197 Children Literature
May 31 2021 I am Not a Troublemaker The Roaring Lion Newcastle 978-1913636159 Children Literature
September 7 2021 Born in Lockdown The Roaring Lion Newcastle 978-1913636289 Poetry
December 31 2021 A god in a Human Body The Roaring Lion Newcastle 978-1913636135 Poetry
July 29 2022 If You Have To Be Anything, be Kind The Roaring Lion Newcastle 978-1913636340 Children Literature
August 14 2022 City of Lost Memories The Roaring Lion Newcastle 978-1913636326 Poetry
September 8 2022 Awaken Your Inner Lion The Roaring Lion Newcastle ' 978-1913636364 Nonfiction
September 8 2022 On The Train To Hell The Roaring Lion Newcastle 978-1913636425 Poetry
January 1 2023 You Need More Than Dreams The Roaring Lion Newcastle 978-1913636302 Poetry
February 28 2023 The Morning Cloud is Empty The Roaring Lion Newcastle 978-1913636388 Poetry
June 22 2023 Architects of a Cleaner Financial System The Roaring Lion Newcastle 978-1913636449 Poetry

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Moyosore, Faith Agboola. "Great blend of themes". The Nation. Retrieved 6 June 2020.
  2. Adebayo, Bukola. "Akinyemi out with Dead Lions Don't Roar". The Punch NG. Retrieved 6 June 2020.
  3. Literary, Review. "Grab Your Chance Now". The Sun: Voice of the Nation. Retrieved 6 June 2020.
  4. Okolo, Edwin. "With "Dead Lions Don't Roar", Tolu Akinyemi opts for relatable simplicity". Ynaija. Retrieved 6 June 2020.
  5. "Amazon Author Central". Amazon Author Central. Retrieved 6 June 2020.
  6. "With Unravel Your Hidden Gems, Tolu Akinyemi digs deep for glory". The Guardian. Retrieved 6 June 2020.
  7. The, Partner. "OkadaBooks For the Weekend Featuring 'Never Play Games with the Devil". Business Day. Retrieved 6 June 2020.
  8. The Newsroom. "Poet to see work in print". New post leader UK. Archived from the original on 6 June 2020. Retrieved 6 June 2020.
  9. Akubiro, Henry (16 September 2017). "Grab your chance now". The Sun (Nigeria).
  10. Akubiro, Henry (23 March 2019). "Wake Up From Your Slumber".
  11. "New book, Dead cats don't meow, hits shelves in April". Vanguard Nigeria. 24 February 2019.
  12. Hållén, Nicklas (2018). "OkadaBooks and the Poetics of Uplift". English Studies in Africa. 61 (2): 36–48. doi:10.1080/00138398.2018.1540152. S2CID 166164213.
  13. 13.0 13.1 "Kolomental and the Elephant in the Room - Our Mental Health. Lecture by Professor Kingsley Oalei Akhigbe". YouTube. 5 October 2023.
  14. Ross, Jordon. "Havering celebrates Black History Month". www.havering.gov.uk (in Turanci). Retrieved 2022-01-29.
  15. Review, The Newcastle (2023-08-03). "Multiple Award-Winning Poet Tolu' A. Akinyemi – The Lion of Newcastle announces North-East Spoken Word Tour for Autumn 2023 – Literary news from the Tyne and beyond" (in Turanci). Retrieved 2023-10-28.
  16. "Events" (in Turanci). Retrieved 2023-10-29.
  17. Tolu' A. Akinyemi performing at Lion and Lilac's Black History Month Special (in Turanci), retrieved 2023-10-28
  18. "New Book Launch Makes Hat Trick For Local Author". Northern Insight UK. Retrieved 6 June 2020.
  19. "Explore University of Hertfordshire Library". University of Hertfordshire Library. Retrieved 6 June 2020.
  20. "Best Indie Book Award". Retrieved 8 January 2021.
  21. "Announcing the 2021 Discovery Awards Winners!". IndieReader (in Turanci). 2021-06-03. Retrieved 2021-06-06.
  22. Awards, Next Generation Indie Book. "Next Generation Indie Book Awards". indiebookawards.com (in Turanci). Retrieved 2021-06-06.
  23. "New book to raise funds for Age UK Northumberland". Northumberland Age UK. Retrieved 6 June 2020.
  24. Northern Insight UK. "Tolu Supports Sunshine Fund". Issue 35. Retrieved 6 June 2020.
  25. Anna, Toms. "Business Book to Raise Charitable Funds". Retrieved 6 June 2020.