Twyse Ereme

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Twyse Ereme
Rayuwa
Haihuwa 28 ga Yuli, 1992 (31 shekaru)
Sana'a
Sana'a Jarumi da cali-cali

Ereme Abraham (an haife shi ranar 28 ga watan Yuli, 1992), an fi saninsa da sunan Twyse ɗan wasan barkwanci ne na Najeriya kuma jarumin Finafinai.[1][2] An fi sanin sa da rawar da yake takawa a Finafinai na barkwanci.[3]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Twyse ya taso ne a garin Ibadan kuma ɗan asalin jihar Edo ne a Najeriya.[4] Twyse ya kasance a cikin ƙasar United Kingdom na ɗan lokaci. A cikin wata hira ta bidiyo da akayi da shi, Twyse ya bayyana cewa yana nazarin doka na ɗan lokaci kaɗan kafin ya daina.[5]

Rayuwa ta sirri da jayayya[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin 2016, akwai labari mai yaduwa game da Twyse yana son kashe kansa. Twyse ya fara tweeting game da tunaninsa na kashe kansa kuma magoya bayansa, abokai da dangi sun damu sosai.[5] Jaruma Toyin Abraham tare da wasu fitattun ‘yan Najeriya sun fara yada bidiyonsa a shafukan sada zumunta da dama. Baya ga wasan barkwanci, Twyse ma mawaki ne. Yana rubuta waƙarsa a lokacin hutunsa.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Americans still want us to be slaves – Twyse". P.M. News (in Turanci). 2020-06-02. Retrieved 2021-07-30.
  2. Features, BellaNaija (2017-10-03). "Becoming a Successful Instagram Comedian in Nigeria". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-07-30.
  3. "2020 100 Most Influential Young Nigerians announced by Avance Media". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2021-07-30.
  4. dnbstories (2020-09-10). "Updated net worth and biography of Instagram comedian Twyse Ereme". DNB Stories Africa (in Turanci). Retrieved 2021-07-30.
  5. 5.0 5.1 BellaNaija.com (2021-07-28). "Bigi x Silverbird Cinemas: Eniola Badmus, Kunle Remi, Tobi Bakre, Uzor Arukwe thrill fans with Cinema Tickets & Rewards". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-07-30.
  6. "Actress in tears as comedian threatens to commit suicide". Pulse Nigeria (in Turanci). 2016-02-18. Retrieved 2021-07-30.