Umar Bin Muhammad Daudpota
Umar Bin Muhammad Daudpota | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tailtiu (mul) , 1 ga Yuni, 1897 |
Mutuwa | Karachi, 22 Nuwamba, 1958 |
Karatu | |
Makaranta |
University of Mumbai (en) Sindh Madressatul Islam University (en) |
Harsuna | Sindhi |
Sana'a | |
Sana'a | Masanin tarihi |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Umar Bin Mohammad Daudpota An (25 ga watan Maris a shekara ta 1896 zuwa shekara ta 22 ga watan Nuwamba 1958) (Sindhi) ya kasance mai bincike na Sindhi, masanin tarihi, masanin harshe kuma masanin Kwarin Indus .
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Daudpota a ranar 25 ga Maris 1896 a shekara ta a garin Talti, Gundumar Dadu, Indiya ta Burtaniya . Yayi karatun farko a garin su Daga bisani, ya yi karatu daga Sindh-Madrasa-tul-Islam" san nan yaje Kwalejin Kimiyya ta D. J. a Karachi, inda ya kanmala digiri sa a BA da MA. Ya ci gaba da karatunsa a kasar Ingila a Kwalejin Emmanuel, Jami'ar Cambridge, inda ya kan mala digiri shi na Ph.D. .
Bayan kammala digirin na Ph.D ya koma ƙasarsa kuma an nada shi a matsayin Shugaban Sind Madrassa . A cikin shekara ta 1930, ya shiga Kwalejin Ismail Yusuf, Bombay, a matsayin farfesa na harshen Larabci. An nada shi Darakta na Koyarwa a Karachi a shekara ta 1939, ya maye gurbin Khan Bahadur Ghulam Nabi Kazi, kuma ya kasance a wannan mukamin har zuwa shekara ta 1948. Gwamnatin kasar Burtaniya ta ba shi taken girmamawa na Shams-ul-Ulama ("Sun of the Scholars").