Jump to content

User:Hassan mdm

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Takaitaccen Tarihin Maitatsine Daga Umar S Ahmad An haifi Marwa Maitatsine a cikin shekarar 1924. Koda yake a iya binciken mu ba mu gano ainihin iyayen Maitatsine ba. Amma bincike ya tabbatar da cewa, Marwa Maitatsine mutumin kasar Kamaru ne. Amma Maitatsinen yana ikirarin cewa shi mutumin kauyen Jabbi ne wacce take cikin tsohuwar jihar Gongola, yanzu jihar Adamawa. Yana boyewa da jihar Gongola ne saboda yadda yake sarrafa harshen Fullanci. Amma da aka zurfafa bincike an gane Maitatsunen shara karya ya yi. Maitatsine dan wani kauye ne mai suna Jappa, a Arewacin Kamaru, garin yana kan iyaka tsakaninsu da Nijeriya. Shi Maitatsine dan kabilar Mufu ne wadanda mafi yawansu ba Musulmai ba ne. Ba su da addini, Maguzanci suke bi. Maitatsine ya shiga addinin Musulunci, a cikin shekarar 1940. A lokacin yana dan kimanin shekaru 16, a duniya. A wancan lokacin ya bar kauyansu ya nufi Marwa. Garin marwa, gari ne na 'yan kabilar Mufu, kafin Fulani su zo su mamaye shi. Shi ya sa Fullanci ya zama shi ne harshen mutanan garin. Har Maitatsine ya kai shekaru 16 yana muguwar al'adar nan ta tsafi, da bautar gumaka, amma Maitatsine bai bar bautar gunki ba, da duwatsu. Suna dinka kambuna da manyan layu. Ga su da irin kau-da-bara, ga sagau, ga su da cin bakin tauri, wuka ba ta kama su. Sukan yanka ma Dodo, Dan Adam, ma'ana su ma sukan zubar da jini. Irin wadannan tsafe-tsafe, da camfe-camfe, Maitatsine ya taso da shi, ya kuma rika yi har da ya zo Kano. Maitatsine, ya fara zama yaron gidan wani Balarabe ne mai suna Mohammad Arab, wanda shi ne ya musuluntar da Maitatsinen. Bayan bayyanar Maitatsine, da yawan mutane sun d'auka sa'a ta yi kusa, tunda "Dujal ya bayyana, rana kawai suke jira ta fito ta yamma, ta fad'i a gabas. Maitatsine bak'i ne tsamurarre mara jiki, tsawonsa zai kai mita 1.7. Sannan ba shi da tsage a fuskarsa, yana da hak'orin gwal guda biyu a bakinsa. Ya sa shi ne a Makka a shekarar 1970. Maitatsine, ya isa Kano ne, cikin shekarar 1955, nan da nan kuma ya kama wa'azi. Bayan farko-farkon samun 'yancin Nijeriya, lokacin ne sha'anin na Maitatsine ya fara ta'azzara. Lokacin hankalin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sunusi ya juyo kan Maitatsine. Sir. Sunusi ya sa aka fidda Maitatsine daga Kano, bai ma tsaya nan ba. Sarkin sai da ya tabbatar da cewa an mai da shi k'asarsu ta Kamaru a cikin shekarar 1962. Bayan da Maitatsine ya koma can k'asarsu ta Kamaru ya ci gaba da yad'a wannan b'arna, yana bad'ala. Bayan Marwa na wancan lokacin Lamido Yaya Hammadi ya kore shi cikin shekarar 1963, ya sake sad'ad'owa Kano, bayan murabus d'in Sir. Sunusi. Ya koma kano da akidar Qur'ani Zalla. Maitatsine yana da'awar shi Annabi ne, kuma yana ganin kansa kamar mujaddidin Shehu Usman Danfodio. Maitasine yana da akidar Qur'ani Zalla, yana inkari ga Hadisi da sunnar Manzon Allah (SAW) kuma yana hani ga karanta wani littafi in ba Qur'ani ba, Maitatsine yana ganin aiki da kayan bature haramun ne kamar su radio, agogo, kekuna, motoci da sauran su. A shekarar 1979, ya fara wannan da'awar ta shi Annabin Hausa ne. A 'yan tsakanin shekarun 1978/1979 ɗin ne 'yan sandan Nijeriya suka sake kama shi. Sannan aka kama yaransa wato Yan Tatsine. Rundunar sojojin Nijeriya ta ba da sanarwan kimanin mutane dubu biyar 5,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin Maitatsine cikin har da shi kanshi Maitatsinen da jama'arsa. Maitatsine ya mutu sakamakon wani rauni da aka yi masa, wasu kuma sun ce ciwon zuciya ne ya kashe shi. A shekarar 2010 jaridar Sunday Trust ta ruwaito gawar maitasine na nan a boye a wajen hukumar 'yan sandan Kano.