Utazi Chukwuka
Utazi Chukwuka | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Enugu North
9 ga Yuni, 2015 - District: Enugu North | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Utazi Godfrey Chukwuka | ||||
Haihuwa | 16 Oktoba 1961 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar Najeriya, Nsukka | ||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Utazi Godfrey Chukwuka CON (an haife shi a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta1961 a Nkpologu, Uzo Uwani dake Najeriya) ɗan siyasar Najeriya ne.[1] Shi ne sanata mai wakiltar mazaɓar Enugu ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.[2][3][4] Sanata ne a majalisar dattawa ta 8 da ta 9 a Najeriya. An fara zaɓen Chukwuka a ranar 9 ga watan Yunin shekara ta, 2015.
Ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar firamare ta Community Primary School Opanda-Nimbo a cikin shekarar 1976; da takardar shedar makarantar sa ta yammacin Afirka (WASC) daga makarantar sakandare ta St. Vincent, Agbogugu a cikin shekarar 1982.
Domin karatunsa na jami’a, da farko ya halarci Kwalejin Ilimi da ke Awka a Jihar Anambra amma ya kammala a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka inda ya samu digirin farko a fannin Gwamnati da Ilimin Siyasa a cikin shekarar 1989. Da yake burin samun ci gaba a fannin sana'a kuma ya san aikin da ke gabansa, sai ya shiga Kwalejin Shari'a ta Jami'ar Najeriya, kuma duk da ƙalubalen da ya fuskanta, ya samu digirin farko a fannin shari'a. Ya halarci Makarantar Shari'a ta Najeriya kuma an kira shi zuwa Lauyoyin Najeriya a shekarar 2004.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Ya ɗauki nauyin wannan ƙudiri na ɗorewar rigakafin cutar shan inna ba wai daga Najeriya kaɗai ba har ma da Afirka.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://punchng.com/enugu-group-moves-to-reconcile-eze-ugwuanyi/
- ↑ https://independent.ng/tribunal-orders-substituted-services-on-ekweremadu-eight-others/
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2018/12/fg-has-proposed-n40m-for-onuiyi-nsukka-erosion-control-sen-utazi/
- ↑ https://thenationonlineng.net/ampion-microsoft-support-200-smes/
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2020/07/polio-senate-wants-immunization-of-children-sustained/