Victor Eletu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Victor Eletu
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 1 ga Afirilu, 2005 (19 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Tsayi 1.7 m

Victor Ehuwa Eletu (an haife shi a ranar 1 ga watan Afrilu shekarar 2005) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ke taka leda a kulob din AC Milan na Italiya U19 .

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Daga Lagos, Nigeria, Eletu ya shafe lokaci yana matashi a Prince Kazeem Eletu Academy a garinsu kafin ya sami gurbin karatu tare da AC Milan a shekarar 2018.

Yin wasa da ƙungiyar 'yan ƙasa da shekara 19 ta Milan, Eletu ya nuna bayyani a kai a kai da farko yana wasa a matsayin ɗan wasan tsakiya mai zurfi a cikin shekarar 2022. A watan Disamba shekarar 2022 ya rattaba hannu kan sabuwar kwangilar shekara biyu da rabi da AC Milan. An daukaka Eletu zuwa matsayin kyaftin din kungiyar U19 a lokacin kakar shekarar 2022-23.

Ayyukan kasa da kasa[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Mayun shekarar 2023 an nada shi a cikin 'yan wasan Najeriya don gasar cin kofin duniya na FIFA U-20 na 2023 .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]