Victor Helu
Victor Helu | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | 6 ga Afirilu, 1983 | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Namibiya | ||||||||||||||||||||||
Mutuwa | 18 Disamba 2009 | ||||||||||||||||||||||
Yanayin mutuwa | kisan kai | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
|
Victor Helu (6 Afrilu 1983 - 18 Disamba 2009) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Namibiya wanda ya taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Civics Windhoek na gasar Premier Namibia da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Namibia. [1] An kashe Helu har lahira a Windhoek a ranar 18 ga watan Disamba 2009.[2]
Helu ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa da ake girmamawa a Namibiya. Ya fara wasan ƙwallon ƙafa na Premier League tare da kulob ɗin Ramblers a shekarar 2002, kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Civics a shekarar 2007. Ya buga wasansa na farko a kulob ɗin Brave Warriors a shekara ta 2002 da Botswana kuma ya ci wa kasarsa wasanni 15. Fitowarsa ta ƙarshe ga kungiyar kwallon kafa ta Brave Warriors ya zo ne a cikin watan Maris 2008 da kasar Malawi. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Victor Helu at National-Football-Teams.com
- ↑ "Victor Helu stabbed to death | Namibia Sport" . Archived from the original on July 22, 2011. Retrieved December 20, 2009.
- ↑ "Victor Helu stabbed to death | Namibia Sport" . Archived from the original on July 22, 2011. Retrieved December 20, 2009.