Wasiƙar Ɓata (fim na 1972)
Wasiƙar Ɓata (fim na 1972) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1972 |
Asalin harshe | Rashanci |
Ƙasar asali | Kungiyar Sobiyet |
Characteristics | |
Genre (en) | comedy film (en) da film adaptation (en) |
During | 79 Dakika |
Direction and screenplay | |
Darekta | Borys Ivchenko (en) |
Marubin wasannin kwaykwayo | Ivan Drach (en) |
'yan wasa | |
Samar | |
Production company (en) | Dovzhenko Film Studios (en) |
Director of photography (en) | Vitali Zimovets (en) |
External links | |
Specialized websites
| |
YouTube |
Wasikar Ɓata wato (The Lost Letter) ( Ukraine , Russian: Пропавшая грамота, romanized: Propavshaya gramota ) fim ne na kasar Ukraine ta Soviet na waka mai dauke barkwanci da al’ajabi wanda aka saki a 1972 wanda Dovzhenko Film Studios suka shirya a Kyiv. An dauki fim din a matsayin lu'u-lu'u na sinimar kasar Ukraine. Fim ɗin ya dogara ne akan labarin novella The Lost Letter: Tale wanda Sexton na N.. . Coci ya bada labari kuma Nikolai Gogol ya rubuta a zagayen 1832 Maraice a cikin Farm Kusa da Dikanka.[1]
Takaitaccen bayani
[gyara sashe | gyara masomin]Cossack Vasyl ( Ivan Mykolaichuk ) ya shirya kansa don tafiya zuwa Peterburg, babban birnin Daular Rasha . Vasyl ya dauki hramota (takardar da aka hatimce) wanda hetman ya ba shi ta hannun sakatarensa Pereverny-Kruchenko, wanda ake yayatawa cewa ta kai farashin akalla taskar gwala-gwalai goma. Matar Vasyl ce ta dinka wannan hramota a kan hularsa, kuma mahaifinsa ( Vasyl Symchych ) ya ba shi taba sihiri don ya kawar da mugunta da shawara don nemo abokin tafiya mai kyau.
‘Yan wasa
[gyara sashe | gyara masomin]- Ivan Mykolaichuk - cossack Vasyl
- Lidia Vakula - Cossack matar, da Empress
- Fedir Stryhun - zaporozhets Andriy, abokin tarayya na cossack
- Zemfira Tsakhilova - Odarka, baroness von Likhtenberg
- Mykhailo Holubovych - mugun mutum (rawar murya actor Pavel Morozenko )
- An gan shi a bangon hoton a matsayin wanda ya mallaki masaukin ( Ukrainian . , korchmar ) a cikin shirin.
- Volodymyr Hlukhyi - m mutum
- Vasyl Symchych - cossack mahaifin
- Anatoliy Barchuk - cossack Ivan
- Volodymyr Shakalo - cossack Petro
- Maria Kapnist - mayya
Matsalolin gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Viktor Hres ya kamata ya zama darrktan shirin, tare da Anatoly Papanov a matsayin jarumin shirin. Amma daga baya, kwatsam sai Hres ya fara rashin lafiya, ya ba jagorancin ga Borys Ivchenko. Daga karshe sun amince akan cewa za a baiwa Ivan Mykolaychuk a matsayin jarumi. An sake rubuta shirin kuma shirya fim din a shekarar 1972 a Dovzhenko Film Studios . Duk da haka, Soviet censors sun hana a tantance shi.[2] Duk da haka, a shekarar 1973 Ofishin Soviet Cinematography propaganda a Moscow ta wallafa ƙasidu guda dubu 50 da hotuna na Ivan Mykolaychuk a matsayin Cossack Vasyl.
A karshe fim din ya fito ne bayan faduwar Tarayyar Soviet. Ya sami lambar yabo ta Golden Pagoda a lokacin bikin fim a Bangkok (duba Cinema na Thailand ). Ivan Mykolaychuk ne ya ba da gudummawa akan dukkannin waƙoƙin da ke cikin fim ɗin, kuma ya taimaka wa Ivan Drach wajen rubuta shirin.[3]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Wasikar da ta ɓace: Labarin Sexton na N.. . Coci (1831), na Mykola Hohol .
- The Lost Letter (1945), Soviet, zane mai ban dariya na harshen Rashanci wanda aka yi fim a Moscow.
- Annychka (1968), wani fim na Borys Ivchenko.
- Cinema na Ukraine
- Dovzhenko Film Studios
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://web.archive.org/web/20200121233234/https://il-journal.com/index.php/journal/issue/download/40/12-2016-pdf. Archived from the original on 21 January 2020. Retrieved 2022-02-03.
- ↑ (PDF) https://web.archive.org/web/20200122000256/http://ekmair.ukma.edu.ua/bitstream/handle/123456789/4501/Bruhoveczka.pdf?sequence=1&isAllowed=y. Archived from the original (PDF) on 22 January 2020. Retrieved 2022-02-03.
- ↑ https://web.archive.org/web/20200122045743/http://www.irbis-nbuv.gov.ua/cgi-bin/irbis_nbuv/cgiirbis_64.exe?C21COM=2&I21DBN=UJRN&P21DBN=UJRN&IMAGE_FILE_DOWNLOAD=1&Image_file_name=PDF/rks_2014_18_34.pdf. Archived from the original (PDF) on 22 January 2020. Retrieved 2022-02-03.