Wikipedia:Gasar Wikipedia20

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Murnar Cikar Wikipedia Shekaru 20

Lokacin gasa: 15 - 22 ga Fabrairu 2021.

Sanar da sakamako: Litinin, 8 ga Watan Maris 2021.

Gabatarwa[gyara masomin]

A ranar 15 ga watan January Wikipedia project yake cika shekara 20 da farawa. An fara shi a 15 ga watan January na 2001. Husa Wikimedians Usergroup yana fatan kasancewa tare da sauran ma'abuta Wikipedia a sauran sassa na duniya domin shirya kwarya-kwaryan biki domin murna da zagayowar wannar rana.

Wikipedia kundin ilimi ce. A cikin shekaru ashirin ta tattara bayanai akan ilimomi da fannonin rayuwa daban daban dan samar da ilimi ga kowa da kowa, da kara habaka nazarce nazarce. Tafi kowane kundin ilimi d aka taba yi yawa, sannan babban madogra ga masu son fara bincike akan wani al'amari. Manufar Wikipedia shine kowane dan'dam yasamu ilimi akan kowane abu batare da biyan wani abu ba o shan wahala a wajen neman wanna bayi.

Wikipedia tayi ƙarko da masana da masu nazarce-nazarce a kanta basu yi tsammani ba. A lokain da aka fara ta mutane da yawa sunyi kirdadon ko zaton bazata kawo wannan lokaci ba, to saidai gashi ta kawo kuma ma har zata wuce.

#Wikipedia20[gyara masomin]

Bikin Wikipedia20 za'ayi shine domin godiya da samuwar wannan kundi mai muhimmancin a garemu, da kuma tattauna abubuwan da ya kamata muyi domin bada tamu gudummuwar domin cigaban wannan ginin da ba mai karewa ba.

Shirye-shirye[gyara masomin]

A Katsina a ranar Asabar 23, ga watan January na shekarar 2021. Akwai link din rajista a https://docs.google.com/forms/d/1iS0HIPay6wwZT580YegchXUh-RqRFHSgD3MBodD6BCA da mutum zai iya yi domin halarta.

Gasa[gyara masomin]

Akwai kwarya-kwaya gasa kuma da za ayi tsakanin 15 zuwa 22 ga watan Fabrairu domin bada kyaututtuka duk acikin wanna bikin nacikar Wikipedia shekara 20.

Ƙa'idoji[gyara masomin]

Akwai wasu muhamman ƙai'doji da za a bi domin kasance a ciki wannan shiri:

  1. Muƙala da aka rubuta cikin salo na daidaito da adalci ba tare da son zuciya ba.
  2. Muƙala da aka rubuta da kyau, a taƙaice, kuma ba tare da kwafin rubutu daga wani wuri ba, ko kuma yawan kurakuran ƙa'idojin rubutun Hausa.
  3. Muƙala da aka rubuta da ingantattu kuma sanannun manazarta kuma a cikin tsari.
  4. Yana da kyau muƙalar ta zama tana da hoton a inda hakan ya dace, ko zai kara sa makaranci fahimtar jigon saƙon.
  5. Dukkan hotuna ya zama an bayyana matsayin haƙƙin mallakarsu, kuma an bayar da bayanin amfanin sa hoton.
  6. An sanya muƙalar a cikin rukunan da suka dace. Yana da kyau a samu aƙalla rukuni guda ukku ko sama da haka.
  7. An bi ƙa'dojin rubutun wikitext ta hanyar amfani da mahaɗa ta ciki da ta waje zuwa wasu shafukan.
  8. Dukkan bayanan da ke cikin muƙalar su zama masu sahihanci, da kuma rubutu mai kyau.
  9. Wanda sukayi rajista kafin rufewa a wurin rajista ne kadai zau iya shiga.

Kyaututtuka[gyara masomin]

  1. . Tablet ta Samsung (ko makamanciya)
  2. . Wayar Huawei Y9 Prime
  3. . Wayar Infinix play.

Sakamakon gasa[gyara masomin]

  1. Na daya - User:Abbasanusi
  2. Na biyu - User:Ibkt
  3. Na ukku - User:Ibraheem Ishola Katsina

Alƙalan gasa[gyara masomin]

  1. . User:Abubakar A Gwanki
  2. . User:M-Mustapha
  3. . User:Ammarpad

Mukaloli[gyara masomin]