Jump to content

Yadda Cossacks ke buga kwallon kafa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Samfuri:Orphan

Yadda Cossacks ke buga kwallon kafa
Asali
Lokacin bugawa 1970
Asalin suna Как казаки в футбол играли
Ƙasar asali Kungiyar Sobiyet
Characteristics
Launi color (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Volodymyr Dakhno (en) Fassara
External links

Yadda Cossacks ke buga kwallon kafa gajeren fim ne na barkwanci na zane daga Kyivnaukfilm studiyo,wanda aka saki a 1970, tana daya daga cikin mafi fitattun shiri kuma labari na biyu a jerin shirin "Cossacks".

Fim din ya fara ne da Cossacks suna jiran dawowar Gray, Oko, da Tur daga Landan. Bayan dawowarsu, ba waii sun bada labaraine game da birnin kawai ba har ma sun gabatar da wasan da suka shaida a can - kwallon kafa.  Sojojin Cossack sun fara horo don lashe kofin kwallon kafa a Ingila. Cossacks guda uku, wadanda suka koya wa wasu mahimman bayanai na kwallon kafa, sun hada wata kungiya kuma suka tafi Turai don buga wasan Cossack March, sun bar makaman su a gida.

Cossacks sunyi wasa a kasashe uku na Turai. Na farko, ƙasar da ba a saka sunanta ba sai dai hanyar allon da ke nuna kalmar "Knights" a lokacin gabatarwar sakamako, mai yiwuwa wakiltar tana nuna 'yan wasa daga Jamus ta zamani. Da farko, Cossacks sunyi gwagwarmaya don karya tsaron knights, suna sanye da makamai. Suna fuskantar jarumawa da hanzari, suna wasa ta hanyar da ke hana abokan adawar su tare da kwallon.

A Faransa, sunyi wasa da 'Yan bindiga (musketeers) a masarauta. Musketeers suna raba kwallo a tsakanin su cikin salo, amma Cossacks sun dogara da matsin lamba bisa ga motsi na raye-raye na mutanen kasar Yukren Hopak kuma sun lashe wasan.

Wasan a Ingila ya faru ne a Landan. Da farko, filin a jike yake saboda ruwan sama, kuma Turawan suna tsaye a kan ƙananan tsibirai, suna raba kwallon a tsakanin su. Daga nan sai Tur ya buga kwallon cikin girgije, ya dakatar da ruwan sama. Filin ya bushe, inda ya ba Cossacks damar zarce Turawa da wasa cikin sauri. Sarauniyar Ingila ta gabatar da su da kofin, wanda Cossacks suka kawo gida.

Kungiyar samarwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rubuce-rubuce

[gyara sashe | gyara masomin]

Samfuri:Infobox film