Yammacin Plateau
Yammacin Plateau shine mafi girman yanki na Australia [1] kuma ya ƙunshi kaso mai yawa na sauran tsohuwar garkuwar dutse ta Gondwana. Ya kunshi kashi biyu bisa uku na nahiyar; yana da kilomita 2,700,000 na busasshiyar ƙasa, wanda ya hada da bangarori masu girma na Yammacin Australia, Kudancin Australia, da Yankin Arewa. Don kwatanta wa, girman sa na kusan dai-dai da duk kan nahiyar Turai daga Poland yamma zuwa Portugal.
Ana samun ruwan sama mara yawa a wannan yankin, kuma ban da ƙananan ramukan ruwa na dindindin, ruwan kasa ba ya samuwa duk kan lokuta sai dai bayan ruwan sama mai yawa. Yawancin yankin yashi ne ko hamada mai duwatsu tare da ƙananun ciyayi.
Matsakaicin ruwan sama a yankin ya sha bambam daga wani yanki zuwa wani yankin, kuma an nakalto shi a millimeters 189 (7.4 in) zuwa millimeters 398 (15.7 in) a kowace shekara, amma ba a iya fadan asalin shi ba.[1]
Dubi kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Garkuwar Australiya
- Babban hamadar Victoria
- Pilbara Craton
- Yilgarn Craton
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Australian Catchment, River and Estuary Assessment 2002". Australian Natural Resources Atlas (ANRA). Archived from the original on 22 August 2008. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "anra" defined multiple times with different content