Yaqub Qureishi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yaqub Qureishi
Rayuwa
Haihuwa 20 century
ƙasa Indiya
Karatu
Harsuna Harshen Hindu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Bahujan Samaj Party (en) Fassara

Haji Yaqoob Qureshi (an haife shi a ranar 5 ga watan Disamban shekara ta 1997) tsohon ɗan siyasa ne na Kasar Indiya kuma memba ne a lardin Uttar Pradesh . An kuma zaɓe shi tsohon MLA na Bahujan Samaj Party.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An zabi Quraishi daga kujerar Meerut a shekara ta 2007 a matsayin dan takarar UPUDF. Bayan wannan ya canza jam'iyyarsa zuwa jam'iyyar Bahujan Samaj Party (BSP). A shekara ta 2012 ya sake canza jam’iyyarsa zuwa jam'iyyar Rashtriya Lok Dal bayan an hana shi tikitin tsayawa takara daga BSP.[ana buƙatar hujja]

Ya shiga zaben shekara ta 2019 na Lok Sabha daga Meerut akan tikitin BSP. Ya kuma sha kaye a hannun dan takarar BJP Rajendra Agrawal . [1] [2]

Rigima[gyara sashe | gyara masomin]

Ya bayar da tukuicin dala miliyan 11 saboda mutuwar masu zane-zanen da suka zana, zane-zanen da ke nuna rashin girmamawa ga Musulunci ko Muhammadu . Bayan harbe-harben da aka yi a shekara ta 2015 a ofishin Charlie Hebdo da ke Kasar Paris, ya sanar da kyautar da za a karba da kudi daga gare shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. http://results.eci.gov.in/pc/en/trends/statewiseS246.htm
  2. https://www.dnaindia.com/elections/lok-sabha-constituencies/meerut-lok-sabha-election-results-2019