Yaren Elgon

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yaren Elgon
Linguistic classification

Harsunan Elgon harsuna ne na dangin Kudancin Nilotic Kalenjin da ake magana da shi a yankin Dutsen Elgon a yammacin ƙasarKenya da gabashin Uganda. A cewar Ethnologue, akwai manyan harsunan Elgon guda biyu: Kupsabiny (wanda kusan mutane kimanin 120,000 ke magana) da kuma Sabaot (wanda kusan bantu 134,000 ke magana). Sabaot sunan gama gari ne wanda mutane daban-daban masu alaƙa suka dukkan ɗauka, gami da Kony, Pok, da Bong'om (wanda aka sanya sunan garin Bungoma na Yammacin ƙazar Kenya), wanda Rottland (1982) ke ɗaukar yarensu daban-daban da ke a yankin.

Mutanen Terik, da ke zaune a gabashin Tafkin Victoria sun shiga tsakanin Nandi, Luo da Luyia, sannan kuma suna magana ko magana da yaren da ke da alaƙa da Pok da Bong'om. Sannan kuma Dangane da tarihin kansu na baki su "mutane ne na Dutsen Elgon"; wannan ya tabbatar da al'adun Bong'om cewa "mutanen da daga baya suka kira kansu Terik har yanzu suna Bong'om lokacin da akan cewa suka bar Elgon kuma suka koma kudu" (Roeder 1986:142). Kwanan nan da yawa daga cikinsu sun dai-daita da makwabciyar Nandi, wanda ya haifar da raguwar amfani da Harshen Terik don amfanin Nandi. Kodayake kuma suna zaune a kasashe biyu, duka kungiyoyin suna magana da yare ɗaya amma tare da ɗan bambancin furci.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]