Yusuf Soalih Ajura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yusuf Soalih Ajura
Rayuwa
Haihuwa Ejura (en) Fassara, 1890
ƙasa Ghana
Mutuwa Tamale, 22 Disamba 2004
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Mai da'awa
Imani
Addini Musulunci

Yusuf Soalih shima ana kiransa Afa Ajura (1890-2004), malamin addinin musulinci ne dan kasar Ghana, mai wa’azi ne, mai rajin siyasa, kuma shine ya kafa kuma ya shugabanci wata kungiya a Ghana. Afa Ajura ya kasance mai goyan bayan musulmin sunna ne da ya guji ayyukan maguzawa na jahiliyya, wanda wasu kuma suka ambace shi a matsayin share fagen kawo canjin akidar wahabiyanci a Ghana. Ya kafa Cibiyar Musulunci ta Anbariyya a Tamale a cikin 1940s. Ya mutu a garin Tamale a ranar 22 ga Disamba, 2004. Saeed Abubakr Zakaria ya gaje shi a 2007 a matsayin shugaban Anbariyya Sunni Community.