Jump to content

Zainab Gimba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zainab Gimba
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Bama/Ngala/Kala-Balge
Rayuwa
Haihuwa Jihar Borno, 25 Disamba 1972 (52 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Zainab Gimba, (an haife ta a ranar 25 ga watan Disamba, 1972) yar siyasan Najeriya ce . An zabe ta a Majalisar Wakilan Na Najeriya a matsayin ‘yar takarar jam’iyya mai mulki ta APC a mazabar tarayya na mazabar Bama / Ngala / Kala Balge, Jihar Borno . Mamba ce a kungiyar mata ta Commonwealth Women Parliamentaries (CWP). kuma mai ba da shawara ga wakilci da kiyaye daidaiton jinsi. kuma tana fafutikan nema ma mata yanci ta bangaren jinsi da kuma daidaito a tsakanin su da maza.[1][2]

Zainab tana da BS.c a cikin Gudanar da Jama'a. Ta kuma kara bunkasa karatunta sannan ta samu digiri na biyu a bangaren mulki. Tana da PhD a cikin Gudanar da Jama'a da Nazarin Manufofi.

Lokacin 2011 zuwa 2014, ta yi aiki a matsayin Hon. Kwamishina Ma'aikatar rage talauci da karfafawa matasa a jihar ta Borno. Ta kuma yi aiki a matsayin Hon. Kwamishina Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Borno daga 2014 zuwa 2015. An nada ta a matsayin Hon. Kwamishina Ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Borno a 2015 kuma ya yi aiki har zuwa 2018.

A yayin taron majalisar dokoki na Commonwealth karo na 64 (CPC) a Speke Resort Munyonyo, Kampala a shekarar 2019, an zabi Zainab a matsayin mataimakiyar shugabar mata ta kungiyar mata ta Commonwealth (CWP) a yankin Afirka.

Lamban girma

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Takardar shedar girmamawa daga Hukumar Kula da Matasa ta Kasa (NYSC) da ke Jihar Yobe saboda karramawar da ta yi a CDS da aikin farko, 2000.
  • Kyautar jagoranci ta ƙwarewa daga ƙungiyar Rotary ta garin Maiduguri, Afrilu 2018
  • Kyautar kyau ta ƙungiyar ɗalibai ta Ngala (NGALSA) don hidimar agaji da ta yi. 29th Afrilu, 2018.
  • Kyauta daga West Africa Water Expo don tallafinta ga Afirka ta Yamma WAWE Expo 2018.
  1. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nassnig.org. Retrieved 7 November 2020.[permanent dead link]
  2. "Nigerian lawmaker elected vice-chairperson Commonwealth Women in Parliament" (in Turanci). 25 September 2019. Retrieved 7 November 2020.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]