Ƙungiyar Haɗin Kan Nakasassu ta Ƙasa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Joint National Association of Persons with Disabilities
Bayanai
Iri umbrella organization (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 1992
masu nakasa

Hadaddiyar Ƙungiyar Naƙasassu ta Ƙasa naja (JONAPWD) ita ce kungiyar da aka kafa a shekara ta 1992 wacce ta haɗa dukkan cibiyoyin nakasassu a Najeriya. Hedikwatar ta ƙasa tana Abuja ne kuma shugabanta na kasa a yanzu shi ne Abdullahi Aliyu Usman. Bangaren ƙasa da ƙasa, ƙungiyar mamba ce ta ƙungiyar naƙasassu ta Commonwealth da ƙungiyar naƙasassu ta Afirka.

Babban ayyukan da suke aiwatarwa ya shafi wayar da kan jama'a game da wanzuwar naƙasassu a duk fadin kasar, da inganta hakkokinsu tare da samar da dokoki da ka'idoji dai-dai da bukatunsu, don shigar da su cikin zamantakewar jama'a na kasa kuma suna tallafawa. bincike kan kalubale daban-daban da matsalolin da suke fuskanta a rayuwar yau da kullun duk abubuwan da ke sama da nufin inganta rayuwar naƙasassu.

Aiyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Daga cikin takamammen ayyukan da suka gudanar a yankunan Najeriya, har da magance wasu kalubalen da masu fama da nakasa ke fuskanta. Misali, sun raka fasinjoji zuwa filayen jiragen saman Najeriya, kamar filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, inda suka bayyana wa jama’a bukatun da mutanen da ke fama da karancin motsi da nakasar ji suke bukata su hau jirgi.

A fagen siyasa shugabannin ƙungiyar sun fito fili sun buƙaci ta kafafen yaɗa labarai da cewa a tsaurara hukunci tare da daure wadanda aka samu da laifin karkatar da kuɗaɗen jama’a da aka tanada domin naƙasassu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]