Abdul-Aziz Ayaba Musah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdul-Aziz Ayaba Musah
Member of the 8th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2021 -
District: Mion Constituency (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Sang, 1 ga Janairu, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Makaranta University for Development Studies (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Abdul-Aziz Ayaba Musah ɗan siyasar Ghana ne kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Mion.[1] An zaɓe shi a lokacin dan majalisa na shekarar 2020, inda ya zama dan majalisa na farko da ya yi nasara akan tikitin New Patriotic Party a mazabar Mion.[2]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1986, kuma ya fito ne daga garin Sang a yankin Arewacin Ghana. Ya yi SSSCE a shekarar 2005. A shekarar 2017 ya samu takardar shaidar kammala digiri a fannin aikin gwamnati sannan a shekarar 2010 ya kara samun digiri a fannin tattalin arziki.[3]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance ma’aikacin bautar kasa a Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa, sannan kuma mai kula da ma’aikatan kananan hukumomi. Shi ne Babban Manaja na Kamfanin Alhaji Musah.[3]

Aikin siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Dan jam'iyyar NPP ne kuma a halin yanzu dan majalisa mai wakiltar mazabar Mion. Ya lashe zaben ne da kuri'u 21,552 yayin da Mohammed Abdul Aziz na jam'iyyar NDC ya samu kuri'u 14,158. Kwace kujerar da Abdul Aziz ya yi ya kafa tarihi domin shi ne karon farko da jam'iyyar NPP ta lashe mazabar Mion cikin shekaru 28.[4][5][6]

A shekarar 2021, an rantsar da Abdul-Aziz tare da Alexander Kwamena Afenyo-Markin, Johnson Kwaku Adu, Laadi Ayii Ayamba da Emmanuel Kwasi Bedzrah a lokacin babban zama na shekarar 2021, na Majalisar ECOWAS wanda ya faru a Freetown na kasar Saliyo.[7]

Kwamitoci[gyara sashe | gyara masomin]

Shi mamba ne na Kwamitin Kasafin Kudi na Musamman sannan kuma memba ne a Kwamitin Samar da Ayyuka, Jin Dadin Jama'a da Kamfanonin Jiha.[3]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Abdul Aziz musulmi ne.[3]

Tallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2020, ya ba da kyautar babur ga Sarkin Jagrido a yankin Arewacin Ghana.[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 26 December 2021.
  2. FM, Peace. "Mion Constituency Results - Election 2020". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 26 December 2021.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-01-16.
  4. "NPP Breaks Record In Mion". DailyGuide Network (in Turanci). 2020-12-15. Retrieved 2022-01-16.
  5. "NPP wins Mion seat for the first time". GhanaWeb (in Turanci). 2020-12-12. Retrieved 2022-01-16.
  6. "Musah Abdul Aziz Ayaba Archives — Kasapa102.5FM" (in Turanci). Archived from the original on 2022-01-16. Retrieved 2022-01-16.
  7. author; ANAETO, Fred (2021-03-29). "1st Extraordinary Session 2021 of ECOWAS Parliament: Adoption of the Strategic Plan (2020-2024) as the first priority". ECOWAS Parliament Website (in Turanci). Retrieved 2022-02-04.
  8. Admin. "NPP Mion Parliamentary Candidate donates to Konkomba Chief | The Custodian Online" (in Turanci). Retrieved 2022-01-16.