An haifi Nasution a ranar 3 ga watan Disamba shekara ta 1918 a ƙauyen Hutapungkut, Mandailing Natal Regency, Arewacin Sumatra, a cikin zuri ‘ar Musulmai a Batak. Shi ne ɗa na biyu zu’ar su kuma ɗan fari. Mahaifinsa ya kasance babban dan kasuwa ne wanda ke sayar da tufafi, roba, da kofi kuma memba ne na kungiyar Sarekat Islam. Mahaifinsa mai addini ne sosai yana son ɗansa ya yi karatu a makarantar addini, kuma mahaifiyarsa yana so yayi karatun a fanin likita a Batavia.kuma bayan kammala karatunsa a makaranta a shekarar 1932, Nasution ya sami tallafin karatu don nazarin koyarwa a Bukitinggi . A cikin shekara ta 1935 Nasution ya koma Bandung don ci gaba da karatunsa, inda ya kasance na tsawon shekaru uku. Muradinsa na zama malami a hankali ya ɓace yayin da samu kan sa a cikin sha'awarsa shiga siyasa . Ya sayi littattafan da ɗan ƙasar Indonesiya Sukarno ya rubuta a asirce kuma ya karanta su tare da abokansa. Bayan kammala karatunsa a shekara 1937, Nasution ya koma Sumatra kuma ya koyar a Bengkulu, yana zaune kusa da gidan da Sukarno ke zaune a gudun hijira. Wani lokaci yakan yi magana da Sukarno kuma ya ji shi yana ba da jawabai. Bayan shekara guda Nasution ya koma Tanjungraja, kusa da Palembang, inda ya ci gaba da koyarwa, amma ya zama mai sha'awar shiga siyasa da kuma aiki soja.[1]