Jump to content

Abdulkareem Mohammad Jamiu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulkareem Mohammad Jamiu
Rayuwa
Sana'a

Abdulkareem Moh'd Jamiu Asuku (an haife shi 2 ga Janairu na shekara ta 1984) ɗan siyasar Najeriya ne. Shine shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Kogi .

Rayuwar farko da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Asuku a Iruvucheba, Okene, Jihar Kogi. Ya samu digiri a fannin haɗa magunguna a shekarar 2009 a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.[1]

An naɗa shi a shekarar 2016 a matsayin Darakta-Janar, Protocol, Gidan Gwamnatin Jihar Kogi a lokacin mulkin Gwamna Yahaya Bello na farko.[2] Ya zama shugaban ma’aikata mafi ƙarancin shekaru a jihar Kogi lokacin da ya naɗa shi shugaban ma’aikatan gwamna a 2019.[3][4] A cikin shekara ta 2020, Asuku ya ƙaddamar da sabis na tallafin kiwon lafiya kyauta ga masu cutar kansa.[5]

Asuku ya tsaya takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress APC domin zaɓen gwamna da za a yi a watan Nuwamba.[6][7]