Abubakar Y. Suleiman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Y. Suleiman
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Abubakar Y Suleiman ɗan siyasan Nijeriya ne wanda aka zaɓa a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ta tara a shekarar 2019.[1][2] Suleiman, dan jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Ningi ne ya kasance zababben kakakin majalisar ta hanyar mambobi 11 daga 31 na majalisar. [3] Daga cikin mambobi 11 da suka zabi Suleiman kakakin, 8 sun kasance mambobi ne na jam'iyyar People's Democratic Party marasa rinjaye yayin da 3 kuma suka kasance 'yan jam'iyyar da suka sauya sheka daga babbar jam'iyyar All Progressives Congress Mambobin jam’iyyar mafi rinjaye (APC) a gidan an hana su shiga harabar majalisar yayin zaben. Wannan kungiyar ta gudanar da nata zaben a wani wuri na daban kuma ta samar da tsohon kakakin majalissar ta 8 Kawuwa Damina wanda ke sake neman takarar kakakin majalisar na tara. [4][5][6] Daga baya an warware rikicin. [7]

A watan Nuwamba na shekarar 2019, an zabi Suleiman a matsayin Shugaban taron shugabannin majalisun dokokin jihohin arewa maso gabas. [8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Alkassim, Balarabe; Bauchi (20 June 2019). "JUST IN: Bauchi Assembly: Suleiman emerges Speaker". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 8 August 2020. Retrieved 26 June 2020.
  2. Gsong (20 June 2019). "BREAKING: Bauchi Assembly: Suleiman emerges Speaker". Republican Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 28 June 2020. Retrieved 26 June 2020.
  3. "Two speakers emerge in Bauchi Assembly". guardian.ng. Retrieved 26 June 2020.
  4. "BREAKING: Two Speakers Emerge In Bauchi Assembly".
  5. "Bauchi Assembly crisis: APC runs to Buhari, IG for help". Businessday NG (in Turanci). 22 June 2019. Retrieved 26 June 2020.
  6. "Court bars National Assembly from interfering in Bauchi Assembly crisis | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 22 July 2019. Retrieved 26 June 2020.
  7. "Bauchi Assembly crisis over —Speaker, Suleiman". Tribune Online (in Turanci). 23 November 2019. Retrieved 26 June 2020.
  8. NewsTimes, Daily (16 November 2019). "Northeast Speakers Elect Bauchi Speaker to Chair Zonal Speakers Conference". Daily NewsTimes Nigeria (in Turanci). Retrieved 26 June 2020.