Adamu Suleiman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adamu Suleiman
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 14 Mayu 1929
Mutuwa 23 Mayu 2005
Sana'a
Sana'a Ƴan Sanda

Adamu Suleiman, An haife shi 14 ga watan Mayun 1929 ɗan sandan Najeriya ne kuma tsohon Sufeto Janar. An naɗa shi a cikin shekarar 1979 don ya gaji Muhammadu Dikko Yusufu sannan Sunday Adewusi ya gaje shi a cikin shekarar 1981.

Suleiman ya halarci makarantar firamare ta Jimeta tsakanin 1940 zuwa 1944, sai kuma makarantar Middle Yola har zuwa shekarar 1947. Sannan ya zama ɗalibi a Kwalejin Barewa da ke Zariya daga shekarar 1947 zuwa 1950, da Kwalejin Fasaha ta Zariya tsakanin 1954 zuwa 1956. Daga nan ya halarci Jami'ar Ibadan, inda daga nan ya kammala karatun digiri a tarihin Zamani a 1960.

An ba shi muƙamin mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya a ranar 1 ga watan Mayun 1966.

Adamu Suleman ya samu muƙamin Sufeto Janar na ƴan sanda a watan Oktoban 1979, kuma ya yi aiki a ƙarƙashin Jamhuriyyar Shugaba Shehu Shagari ta biyu har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga aikin ƴan sanda a watan Afrilun 1981.[1][2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Akinsanya, Adeoye A.; Ayoade, John A. A. (2005). Readings in Nigerian Government and Politics. Gratia Associates International. p. 244
  2. https://thenationonlineng.net/arase-idris-police-chief/