Adeyemi Afolayan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adeyemi Afolayan
Rayuwa
Haihuwa Kwara, 1940
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 1996
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi, marubin wasannin kwaykwayo da darakta

Adeyemi Afolayan

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Afolayan a shekarar 1940 a jihar Kwara ta Najeriya.[1] Dan uwa ne ga jaruma Toyin Afolayan kuma mahaifin jaruman fina-finai Kunle Afolayan, Tayo Afolayan, Gabriel Afolayan, Moji Afolayan, da Aremu Afolayan. [2] [3]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1966, Afolayan ya shiga kungiyar wasan kwaikwayo ta Moses Olaiya, a shekarar 1971, ya tashi ya kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo ta kansa wadda ta rika gudanar da wasannin barkwanci. [4]

A shekarar 1976, ya fito a Ajani Ogun na Ola Balogun, daga baya kuma ya fito da fim din Ija Ominira (1979), kuma Balogun ne ya bada umarni. Kadara, wanda kuma ake kira Destiny a turance shine fim na farko da ya rubuta, ya shirya kuma ya fito a matsayin babban jarumi. An nuna fim din a bikin fina-finan Tashkent karo na tara na fina-finan Afirka da Asiya. Afolayan ya ci gaba da shiryawa da tauraro a sauran shirye-shirye kamar Ija Orogun, Direban Tasi da Iya ni Wura. [5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Dad didn't encourage his children to act —Kunle Afolayan".
  2. "Saying I'm beautiful is flattery". Nigerian Tribune
  3. "FAMILY REMEMBERS VETERAN YORUBA FILMMAKER, ADE LOVE 20 YEARS AFTER DEMISE".
  4. Timothy-Asobele, S. J. (2003). Yoruba cinema of Nigeria. Lagos, Nigeria: Upper Standard Publications
  5. Timothy-Asobele, S. J. (2003). Yoruba cinema of Nigeria. Lagos, Nigeria: Upper Standard Publications