Jump to content

Alhaji Hassan Dalhatu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alhaji Hassan Dalhatu
Rayuwa
Haihuwa 31 Disamba 1936 (87 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
hoton gangami a masarauyar zazau da alahaji
alhaji hassan a masarautar zazau

Hassan Ɗalhat, (an haife shi ranar 31 ga watan Disamba, shekarar 1936) a unguwar Kakaki a tsohon birnin Zariya. Gogaggen ma'aikacin gwamnati ne kuma mai gudanarwa wanda ya yi aiki a matakin sama na ma'aikatan gwamnatin jihar Kaduna. Ya riƙe sarautar gargajiya ta Cigarin garin Zazzau (Mai nasara) kuma Hakimin Sabon Birnin Daji a jihar Kaduna. Da na 3 kuma na ƙarshe ga marigayiya Hajiya Fatima Dalhatu (1905-1998) da ta bakwai zuwa marigayi Alkali Dalhatu Muhammad (1885-1956). Mahaifinsa babban Alƙali ne mai daraja kuma mai faɗa a ji (Alƙali) wanda ya yi aiki a Anchau-Takalafiya da Maƙarfi a jihar Kaduna. Bayan rasuwar Shehu Ladan (tsohon GMD na NNPC kuma na farkon Cigarin Zazzau), Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr) Shehu Idris ya karrama shi da babbar karrmawa. A matsayinsa na Hakimin Lardi, ya kasance majiɓincin Ilimin Addinin Musulunci da na zamani (Ilimin boko) a matsayin hanyar samun nasara a Najeriya ta zamani. Shi shugaba ne mai kishin al'umma wanda ba ya tunanin kan sa da kuma wanda ba shi da gata. Bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 1956, babban yayansa Alkali Bashir Dalhatu ya zama waliyinsa, yayin da Marigayi Maccido Dalhat CON (1932-2012) ya zama mai ba shi shawara, amana kuma mai kare shi. Cigarin Zazzau yanada mata 3 da ƴaƴa goma.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • www.leadership.ng/nga/articles/18644/2012/03/09
  • africafocus.com/2012/03/09/tambuwal
  • Alhaji Shehu Idris, The 18th Emir of Zazzau
  • Zuriyar Mallam Ibrahim Tsoho dake Kakaki a cikin birnin Zaria, Na Dr Dogara Bashir.