Jump to content

Ambaliyar Ruwa n Jihar Benue ta 2017

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ambaliyar Ruwa n Jihar Benue ta 2017
ambaliya
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata Satumba 2017
Has cause (en) Fassara Ruwa mai karfi a Najeriya
Yana haddasa ambaliya
Lambar aika saƙo 981113
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Benue
Taswirar annaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa ta 2017 a jihar Benue, ta faru ne a cikin watan Satumban 2017 a jihar Benue dake Najeriya. [1] Ta raba a ƙalla mutane 100,000 da muhallansu, [2][3] ta lalata gidaje sama da 2,000.[4]

An shafe tsawon makonni ana sheƙaƙa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, da magudanun ruwa da kuma koguna a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya. Ƙananan hukumomi guda 21 a cikin guda 23 da ke jihar Binuwai abin ya shafa. [5] Ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare a yankin sakamakon mamakon ruwan sama da kuma kogin Binuwai da ke ratsa yankin.

Illoli kan sauyin yanayi

[gyara sashe | gyara masomin]

Ambaliyar ta yi kama da ta shekarar 2012 mai tsanani. Ambaliyar dai ta rutsa da manyan gada biyu a kan kogin Guma a Tor Kpande da Mande Ortom. An kuma lalata gonaki da rumbunan abinci a cikin al'ummomin da abin ya shafa. Sabbin hanyoyin Daudu-Gbajimba da aka gina, da Jami'ar noma ta Makurdi, ba su tsira ba saboda ba za su iya wucewa ba bayan da ruwa ya yi awon gaba da waɗansu sassan titunan. [6] Noma a Benue na fuskantar ƙalubale da dama waɗanda ke barazana ga makomar noma. Ƙarfin ruwan sama kamar yana ƙaruwa tare da raguwa a hankali. Matsakaicin fitarwa a tashar ruwa ta Makurdi ya kai 3468.24 m³s⁻¹, kuma mafi girman fitarwar ya kai 16,400 m³s⁻¹. Matsakaicin zafin rana da matsakaicin zafin jiki na shekara suna tashi a hankali, yana haifar da ƙarin zafi. Bincike ya nuna cewa ƙasa tana da ɗanɗano kaɗan amma tana buƙatar ingantaccen amfani da takin inorganic da na halitta. Babban ayyukan yi da sana'a a yankin sun dogara ne a kan noma.[7]

  1. "More than 100,000 displaced by flooding in central Nigeria". USA TODAY (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-12. Retrieved 2018-10-03.
  2. "Nigeria – Thousands Displaced by Floods in Benue State – FloodList". floodlist.com (in Turanci). Copernicus. 5 September 2017. Retrieved 2017-09-10.
  3. Al Jazeera (1 September 2017). "Nigeria floods displace more than 100,000 people". www.aljazeera.com. Retrieved 2017-09-10.
  4. "Flood Hits Makurdi, Ravages Over 2,000 Homes • Channels Television". Channels Television. 2017-08-27. Retrieved 2017-09-10.
  5. "West and Central Africa: 2017 flood impact". Reliefweb 18 Oct 2017.
  6. "Benue flood: Gov Ortom raises the alarm". Vanguard. October 14, 2022. Retrieved September 3, 2017.
  7. Abah, Roland Clement; et al. (December 2016). "Assessment of potential impacts of climate change on agricultural development in the Lower Benue River Basin". National library of Medicine.