Jump to content

Angel Gnonsoa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Angel Gnonsoa
Rayuwa
Haihuwa 1940 (83/84 shekaru)
ƙasa Ivory Coast
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Mamba Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Ivory Coast.
Imani
Jam'iyar siyasa Ivorian Workers' Party (en) Fassara

Angèle Gnonsoa ko Angèle Gnonsoa Zonsahon (an haife ta a shekara ta 1941) malama ce kuma 'yar siyasa 'yar ƙasar Ivory Coast.[1] Ta kasance Ministar Muhalli daga shekarun 2003 zuwa 2005, kuma Ministar Ilimin Ma'aikata a lokacin rikicin 2010-2011 na Ivory Coast.

Angele Gnonsoa ta sami horo a matsayin kwararriya a fannin ilimin ɗan adam, tana karatu a Faransa.[1] Tana magana da yaren Wè, Gnonsoa ta yi bincike kuma ta koyar da al'adun baka a Jami'ar Abidjan.[2] Ita ƙwararriya ce akan amfani da abin rufe fuska (Marks) a Wè festivity.

A matsayin na malamar jami'a Gnonsoa ta yi aiki tare da Francis Wodié, tana ƙoƙarin tabbatar da siyasar jam'iyyun siyasa a Ivory Coast. Ta kasance memba ta kafa jam'iyyar Ma'aikata ta Ivory Coast (PIT) a cikin shekarar 1990. Ita ce sakatariyar PIT ta ƙasa ta biyu, sannan kuma ta zama mataimakiyar shugaban jam'iyyar ta farko. Daga shekarun 2003 zuwa 2005 ta yi aiki a matsayin Ministar Muhalli, ta wakilci PIT a gwamnatin Seydou Diarra ta haɗin kan ƙasa bayan yakin basasa na farko na Ivory Coast.[1]

Bayan zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasar Ivory Coast a shekara ta 2010 a watan Oktoban shekarar 2010, jam'iyyar ma'aikata ta Ivory Coast ta samu rarrabuwar kawuna kan ko wanene daga cikin 'yan takarar da ke kan gaba za su marawa baya. Gnonsoa ta yi adawa da Wodié, wanda ya so ya goyi bayan gamayyar dama ta tsakiya ta Alassane Ouattara. Gnonsoa ta zaɓi ya goyi bayan Laurent Gbagbo, kuma bayan zaɓen da aka yi ta cece-kuce, ta shiga gwamnatin Gbagbo a ƙarƙashin Gilbert N'Gbo Ake a matsayin ministar ilimi na kwararru. Bayan kama Ggagbo a watan Afrilun 2011, an kuma kama Gnonsoa. Ko da yake ta tsere daga gidan yari, tana bukatar barin Ivory Coast, inda ta yi zaman gudun hijira a Ghana na tsawon shekaru takwas har sai ta koma Ivory Coast a shekara ta 2019.[3]

  • (With Philippe Oberlé) Masques vivants de Cote d'Ivoire. Colmar, France: SAEP, 1985.
  • Le masque au cœur de la société wè . Abidjan: Frat Mat editions, 2007.
  1. 1.0 1.1 1.2 Cyril K. Daddieh (2016). "Gnonsoa, Angèle". Historical Dictionary of Cote d'Ivoire (The Ivory Coast). Rowman & Littlefield. pp. 271–2. ISBN 978-0-8108-7389-6.
  2. African Arts. African Studies Center, University of California, Los Angeles. 1992. p. 106.
  3. "Ivorian Former Ministers in Ghana Return Home After 8 Years in Exile". UNHCR. 5 February 2019. Retrieved 21 February 2021.