Anne Aasheim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anne Aasheim
Rayuwa
Haihuwa Porsgrunn (en) Fassara, 22 ga Afirilu, 1962
ƙasa Norway
Mutuwa 30 ga Maris, 2016
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji)
Ƴan uwa
Ahali Erik Aasheim (en) Fassara
Karatu
Harsuna Norwegian (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da editing staff (en) Fassara
IMDb nm8924578

Anne Aasheim (22 Afrilu 1962 - 30 Maris 2016) edita ce ƴar ƙasar Norway.

Farkon rayuwa da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a Porsgrunn kuma ta fara aikin jarida a babban gidan jaridar birnin Varden a ƙarshen 1970s. Ta yi aiki a Dagen da Bergens Arbeiderblad kafin a dauke ta aiki a NRK Hordaland a 1988.[1]

Darekta[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi aiki a matsayin darekta na rikon kwarya a NRK P3 a Trondheim da NRK P2 a Oslo kafin a nada ta a matsayin darektan gidan labarai na Østlandssendingen a 1997. A shekarar 1999 ta yi aiki a matsayin mukaddashin darektan al'adu a kamfanin dillancin labarai, kafin ta zama darektan labarai na kasa da na gundumomi daga 2001 zuwa 2005. Bayan wani lokaci a matsayin babbar editan Dagbladet daga 2006 zuwa 2010, ta yi murabus kuma ta zama sabuwar manajan darakta na Majalisar Arts Norway a 2011.[1]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi aure da mai bincike Mette Tollefsrud, tayi rayuwa a Ila, Oslo.[2]

Dalilin Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Aasheim ta mutu sakamakon cutar kansar huhu a Oslo a cikin shekarar 2016.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Anne Aasheim". Store norske leksikon (in Norwegian). Retrieved 17 February 2014.
  2. Valle, Viggo; Mølster, Elisabeth Strand; Johansen, John Magne (19 January 2009). "Anne Aasheim" (in Norwegian). Norwegian Broadcasting Corporation. Retrieved 17 February 2014.
  3. "Anne Aasheim er død". 30 March 2016.
Template:S-mediaTemplate:S-culture
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}