Jump to content

Anthonia Fatunsin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anthonia Fatunsin
Rayuwa
Cikakken suna Anthonia Kehinde Fatunsin
Haihuwa 20 century
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a archaeologist (en) Fassara
Employers National Museum of Unity


Anthonia Kehinde Fatunsin ƙwararriya ce kuma masaniya a fannin ilimin kimiyya na kayan tarihi ta Najeriya. Ana yi mata kallon mace ta farko a Najeriya, kuma mace ta farko da ta shugabanci gidan kayan tarihi na Ibadan.[1] Aikinta ya ta'allaka ne akan tukwane na yoruba, musamman daga al'ummar Owo.[2]

Binciken archaeological

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1981, Fatunsin ta fara aikin tonon Igbo'laja da Ijebu-Owo a cikin garin Owo domin gano abin da ake kira Owo terracotta. Babasehinde Ademuleya daga Jami’ar Obafemi Awolowo ta bayyana cewa jarrabawar da ta yi ita ce karo na biyu da ake tono garin bayan ziyarar Ekpo Eyo a shekarar 1976. Duk da haka, ana lura cewa Fatunsin ita ce ta farko da ta ba da cikakken bayani game da halaye na sassaka.[3]

Aikin Ilimin kayan tarihi

[gyara sashe | gyara masomin]

Fatunshin ta yi rubuce-rubuce game da rawar da ilimin kimiya na kayan tarihi ke takawa a gidajen tarihi na Najeriya da kuma tasirinsa ga kayan tarihi a ƙasar.[4] An gane ta a matsayin majagaba na tunani da fassarar kayan tarihi na bayan mulkin mallaka a Afirka.[5]

  1. Oziogu, Apollos Ibeabuchi (17 June 2012). "Owo culture of ancient Nigeria". Vanguard. Retrieved 2021-06-09.
  2. "Fatunsin, Anthonia". WorldCat. Retrieved 2018-04-02.
  3. Babásèhìndé, Adémúlèyá (July 2015). "Stylistic Analysis of Igbo 'Laja Terracotta Sculptures of Owo". Mediterranean Journal of Social Sciences. 6 (4 S2). Retrieved 2021-07-01 – via mcser.org.
  4. Fatunsin, Anthonia K. (1994). "Archaeology and the protection of cultural heritage: the Nigerian situation". Archéologie et sauvegarde du patrimoine: Actes du VIe colloque, Cotonou, Bénin, 28 mars - 2 avril 1994 = Archaeology and safeguarding of heritage: Proceedings of the 6th colloquium, Cotonou, Benin, 28th March - 2nd April 1994 (in Turanci): 63–69.[permanent dead link]
  5. Theory in Africa. doi:10.4324/9781315716381-7. ISBN 9781315716381. Retrieved 2019-11-14.