Asiya Abdullahi
Asiya Abdullahi (chairlady) jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood tana hawa waƙoƙin soyayya tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suka iya rawa.[1]a masana'antar.
Takaitaccen Tarihin Ta
[gyara sashe | gyara masomin]Cikakken sunan ta shine Asiya Abdullahi Amma anfi sanin ta da Asiya Chairlady ko Kuma sunan da ake kiran ta dashi wato Cyleeder. An haife ta a ranar 11 ga watan Maris a shekara ta alif dari tara da casa'in da uku miladiyya 1993. Tayi karatun firamare da Sakandire a garin Kano. Anyi rikon ta a Jihar Kaduna a cikin garin Zariya. Daga baya ta dawo Jihar Kano tare da Yan uwanta. Har ta sami shiga masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud.
Masana'antar fim
[gyara sashe | gyara masomin]Asiya ta shigo masana'antar a shekarar 2014 amma Bata fito a fina finai da yawa ba sedai waka. Ta iya rawa sosai shiyasa wakokin nata ke shiga sosai. Tayi wakoki da manyan jarumai kamar su Adam A Zango, Salisu S Fulani, da Kuma kananun jarumai masu tasowa.[2]
Fina finan data fito
[gyara sashe | gyara masomin]- Attajiri
- Fansa
- Amfanin hankali
- Na malle
- zaman marina
- Murfi
- Abubakar sadiq
- Da sauran su