Jump to content

Ayyukan da ke tauye ladan mai azumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sham ruwa lokacin Azumi a Indonesiya

Azumi A cikin Musulunci, azumi (wanda aka fi sani da sawm,[1] [1] Larabci: صوم; lafazin Larabci: [sˤawm] ko siyam, Larabci: صيام; lafazin Larabci: [sˤijaːm], wanda aka fi sani da rūzeh ko rōzah (Persian: روزه) a cikin wadanda ba -Ƙasashen Musulmi na Larabawa) al'ada ce ta kamewa, yawanci daga abinci, sha, jima'i da duk abin da ya maye gurbin abinci da abin sha. A cikin watan ramadan ana yin sahur ne tsakanin ketowar alfijir zuwa dare a lokacin da ake busa sallar magriba[2]. Watan Ramadan wata ne na tara a cikin kalandar musulmi, kuma azumi abin bukata ne ga musulmi kasancewar shi ne na hudu daga rukunnan Musulunci guda biyar.[2][3]

Abun da ke rage ladan azumi[gyara sashe | gyara masomin]

Azumin Ramadan lokaci ne da al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke zage damtse domin yin ayyukan da za su inganta imaninsu tare da kyautata wa ƴan uwa da abokan arziki duk saboda neman tsira da samun lada.

Watan azumi lokaci ne da Allah ubangiji yake ninka ladan ibadu da mutane ke yi.

Harwayau, azumi na ɗaya daga cikin rukunai biyar na addinin Musulunci, kuma a a watan ne aka saukar wa Manzon Allah (SAW) Al-Qur'ani Mai Girma.

BBC ta tuntuɓi Malamin addinin Musulunci, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya da ke birnin Kaduna, kuma ya yi bayani kan abubuwan da ke cinye ladan mai azumi kamar haka:

Yin karya da zantuka marasa amfani - Malamin ya ce yawaitar yin karya ko yi wa wani barazana na cikin abubuwan da ke rage ladan azumi. Yi da mutane na rage ladan azumi. Yawan yin surutan banza Guje wa abin da zai tayar da sha'awa Kiyaye harshe daga faɗar zantuka marasa alheri Sheikh Halliru Maraya ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su kiyaye dokokin Allah, musamman a wannan lokaci na azumi.

"Duk abin da Allah ya ce a aikata, a aikata daidai gwargwado. Duk abin da ya ce a nisanta, to a nisanta baki-ɗaya," in ji Malamin.

Ya kuma yi kira ga ƴan kasuwa da su yi kokarinsu wajen rage farashin kayayyakinsu da bin riba ƴar kaɗan.

Ya ce ya kamata su rika yi wa mutane sauki idan sun je sayen kayayyaki musamman a cikin wannan wata na azumi.

"Ina kira mu zauna lafiya tsakaninmu mu Musulmi, sannan kuma mu zauna lafiya har da abokanmu waɗanda ba Musulmi ba.[4]

Abubuwan da ake son mai azumi ya lazimta[gyara sashe | gyara masomin]

Cikin abubuwan da Malamin ya ce suna ƙara lada a wannan wata na azumi sun haɗa da:

Yawaita karatun Al-Kur'ani: Malamin addinin Musuluncin ya ce yawaita karatun Al-Qur'ani mai girma a wannan lokaci na azumi yana haɓaka lada saboda falalarsa.

Yawaita zikiri: Sheikh Halliru Maraya ya kwaɗaita wa mutane cewa su yawaita yin zikiri kamar istigfari da salatin annabi da hailala da kuma yawan tasbihi.

Yawaita ciyarwa: Malamin ya kuma ce ciyarwa a wannan lokaci na azumi ba karamin abu ba ne saboda falalar da ke tattare da hakan. Ya ce Manzon Allah (SAW) ya kwaɗaitawa mutane muhimmancin ciyarwa.

"Ya kamata mu kwaikwayi irin yadda ƙasahe kamar Saudiyya ke samar da abinci irin nasu domin ciyarwa. Mutane za su iya haɗa karfi domin ciyar da masu azumi," in ji Sheikh Halliru Maraya.

Sallar dare: Sheikh Maraya ya ce wani abu da ke haɓaka lada a watan azumi shi ne yawaitar nafilolin dare musmaman tahajjud da sallar tarawihi saboda falalar yin haka ba ta misaltuwa.

Kame baki: Malamin ya ce mai azumi ya kasance yana kame baki daga yin karairayi saboda hakan na janyo tawaya ga azumi. Ya ce ko da mutum ba ya azumi karya haramun ce a gare shi.

"Haka kuma kame baki daga yi da mutane, misali irin yadda mutane ke zama a bakin hanya suna yi da duk wanda ya wuce, duka ya kamata a kiyaye," in ji Malamin.

Halartar wuraren tafsiri: Sheikh Halliru ya ce mutane su rika bayar da lokacinsu wajen halartar tafsirai da kuma jin sakon Allah, inda ya ce hakan zai bai wa mutum damar sanin abubuwan da Allah yake so da wadanda ba ya so.

Ziyarar asibitoci da gidajen yari: Wane abu kuma da Malamin ya ce na ɗaya daga cikin hanyoyi na samun lada shi ne ziyarar asibitoci da kuma gidajen yari domin taimakawa bayin Allah.

"Ziyarar asibitoci da gidajen yari na da muhimmancin gaske kuma hanya ce ta samun lada sosai. Tallafawa masu kula da marasa lafiya da kuma su marasa lafiyan da likitoci suka ba su damar yin azumi zai haɓaka ladar mutum matuka.

"Mutane za su iya haɗa-kai wajen kai kayan tallafi domin raba wa Musulmai da ke gidajen yari wajen ganin sun samu abincin buɗe-baki da kuma sahur," in ji Sheikh Halliru Maraya.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Islam". HISTORY. Retrieved 2020-01-24.
  2. "Islam - Prayer". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2020-01-24.
  3. https://en.wikipedia.org/wiki/Fasting_in_Islam
  4. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp6dj54552do
  5. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp6dj54552do