Jump to content

Barmani Choge

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Barmani Choge
Rayuwa
Haihuwa 1945
ƙasa Najeriya
Mutuwa Funtua, 2013
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Barmani ChogeAbout this soundBarmani choge  asalin sunanta Sa'adatu Aliyu (an haife ta a shekara ta alif 1943) 'yar asalin garin Funtuwa, Jihar Katsina Najeriya ce. shahararriyar mawakiya ce, mai kiɗan ƙwarya ko kiɗan amada. Ta fara waƙa tana da shekara 27. Waƙar Amada ta samu karɓuwa da yaduwa sanadiyar Barmani Choge, ganin irin tashe da ta yi a cikin harkar waƙar, kuma hakan ya sa ta zama mafi ɗaukaka a cikin mata masu waƙa na Arewacin Najeriya. Waƙoƙinta suna faɗakarwa ga mata a kan neman ilimi, da yin sana'o'in hannu da kuma nunin illar zaman kashe wando, ta hanyar raha da yin tsokana a kan kishiyoyi a gidan aure. Choge dai ta rasu a shekara ta 2013, sakamakon cutar ciwan suga wacce tai sanadin mutuwar sahen jikinta, tana yar shekara 70 da haihuwa. Ta bar 'ya'ya shida 6 da jikoki sittin 60.[1][2]

  1. Abdalla Uba Adamu, 'Tribute to Hajiya Sa’adatu Ahmad Barmani Choge, Griotte, northern Nigeria, 1948-2013', The Annual Review of Islam in Africa, Issue No. 12/13 (2015-16), pp.166-172.
  2. Umma Aliya Musa (2020). "Promoting women empowerment through songs: Barmani Choge and her performances". Journal of African Languages and Literature. 1: 89–101.